Kano: Bajiman Lauyoyi Sun Yi Watsa-Watsa da Hukuncin Alkalai a Shari’ar Abba v Gawuna

Kano: Bajiman Lauyoyi Sun Yi Watsa-Watsa da Hukuncin Alkalai a Shari’ar Abba v Gawuna

  • Kabir Akingbolu esq ya tofa albarkacin bakinsa game da hukuncin da kotun sauraron karar zabe ya yi a shari’ar Gwamnan Kano
  • A matsayinsa na masanin shari’a kuma mai hare hakkin jama’a, lauyan ya ce Alkalan kotun sun yi kura-kurai da-dama a hukuncinsu
  • Akingbolu ya ce abubuwa za su kara fitowa fili a kotu musamman bayan hukuncin da aka zartar a shari’ar zaben shugaban kasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Maganar shari’ar zaben Gwamnan Kano a 2023 ta dawo yayin da ake shirin fara sauraron karar a kotun daukaka kara a yau Litinin.

A wata hira da aka yi da Kabir Akingbolu esq, ya nuna kotun korafin zabe ta yi kuskure wajen soke nasarar da INEC ta ba Abba Kabir Yusuf.

Kara karanta wannan

Kano: Kotun Daukaka Kara Ta Yi Hukunci Kan Shari'ar Zaben Dan Majalisar Tarayya, Ta Fadi Mai Nasara

Lauya kuma mai kare hakkin Bil Adama, Kabir Akingbolu ya shaidawa tashar TVC cewa ba ayi adalci wajen yanke hukuncin zaben Kano ba.

Abba v Gawuna
Kotu ta ba Gawuna nasara a kan Abba a Kano Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lauya ya ce babu adalci a shari'ar zaben Kano

A cewar Lauyan, Alkalan da su ka yi hukunci sun bar filin daga ne sun shiga cikin jeji a hukuncin da su ka zartar da ta ba APC nasara a Kano.

"Maganar gaskiya kenan, kotun sauraron karar zabe ta yi wasu kwan-gaba-kwan-baya.
A wata gabar shari’ar, kotun ta ce ba ta da hurumin duba dalilin kin sa hannu a takardun kada kuri’a, daga baya ta ce ta na da hurumin hakan.
Kotun ta duba takardun da aka gabatar wanda babu wani shaida da ya ce uffan a kan su, sannan ta ce ba a jibge mata takardu haka kurum.

Kara karanta wannan

Babu maganar komawa Majalisa bayan Ministar Tinubu ta fado ta kai a Kotun zabe

- Kabir Akingbolu

Hukuncin shari'ar Kano ya sabawa kotun koli

Kamar yadda ya yi bayani a rubutunsa a Sahara Reporters, Akingbolu ya ce akwai cin karo a dogara da Alkalan zaben su ka yi da dokar zabe.

Akingbolu ya ce dokar amfani da hujjoji ya kamata kotu ta duba ba sashe na 137 na dokar zabe ba, akasin Alkalan kotun koli su ka yi a bana.

A lokacin da kotun karar zaben ta yi wannan hukunci ta kafar Zoom, Lauyan ya ce kotun koli ba ta saurari karar zaben shugaban kasa ba tukun.

Masanin ya na ganin hukuncin da kotun koli ta yi tsakanin Atiku, Obi da Tinubu ya tabbatar da ana bukatar shaidu kafin a soke nasarar NNPP.

Ra'ayin Falana a shari'ar Gwamnan Kano

Shi kuwa Femi Falana SAN wanda sunan shi ya zaga ko ina, ya yi Allah-wadai da hukuncin da aka yi a kan shari'ar zaben Gwamnan na Kano.

Fitaccen lauyan ya ce babu dalilin da kotu za ta azabtar da al'ummar Kano ta hanyar ruguza nasarar NNPP saboda sakacin INEC a takardun zabe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng