Yaudara Ko Don Allah? Yahaya Bello Ya Ware Miliyan 497 Don Dalibai Ana Saura Kwanaki 6 Zabe a Jihar

Yaudara Ko Don Allah? Yahaya Bello Ya Ware Miliyan 497 Don Dalibai Ana Saura Kwanaki 6 Zabe a Jihar

  • Yayin da ake saura kwanaki a gudanar da zaben gwamnan jihar Kogi, Gwamna Yahaya Bello ya yi bajinta a jihar
  • Gwamnan ya ware naira miliyan 497 don biya wa dalibai fiye da dubu 15 kudin jarabawar WAEC a jihar
  • Wannan na zuwa ne yayin da ake shirye-shiryen gudanar da zaben gwamnan jihar a ranar 11 ga wannan watan

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kogi – Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi ya amince da biyan naira miliyan 497 na jarabawar WAEC ta 2023 ga dalibai a jihar.

Wannan na zuwa ne ana saura kasa da kwanaki bakwai a gudanar da zaben gwamnan jihar.

Yahaya Bello ya biya kudin jarabawar WAEC ga dalibai ana saura kwanaki 6 zabe
Gwamna Bello na jihar Kogi ya biya wa dalibai kudin jarabawar WAEC. Hoto: Yahaya Bello.
Asali: Facebook

Mene Yahaya Bello ya yi a Kogi?

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP da kujerarsa ke tangal-tangal ya nemi afuwar talakawan jiharsa kan abu 1 da ya faru

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren yada labarai na gwamnan, Onogwu Mohammed ya fitar, cewar Channels TV.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta ce:

“A kokarinsa na inganta harkar ilimi, gwamnan ya fitar da naira miliyan 497 don dalibai ma su rubuta jarabawar WAEC a jihar.
“Har ila yau, wannan na daga cikin kokarin gwamnatin jihar na samar da ilimin firamare da sakandare kyauta a jihar.”

Dalibai nawa za su moriyar ta Yahaya Bello a Kogi?

Onogwu ya ce daga cikin makarantun kananan hukumomin da za su fi cin gajiyar kudaden jarabawar akwai Dekina da ke da mafi yawan dalibai har 1,867.

Sannan sai karamar hukumar Lokoja da dalibai 1,569 da Okene dauke da dalibai 1,345, cewar Vanguard.

Ya kara da cewa wannan hobbasa na gwamnan zai shafi dalibai akalla 15,033 a jihar don inganta mu su harkokin ilimi.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Malam Dikko ta bankaɗo wasu illoli da ƴan bindiga suka yi a Jihar Katsina

Kungiya ta bukaci kama Melaye kan zargin ta’addanci

A wani labarin, wata kungiyar kare hakkin dan Adam ta bukaci jami’an tsaro su cafke Dino Melaye kan zargin ta’addanci a shekarar 2007 a jihar.

Kungiyar ta ce dan takarar na jam’iyyar PDP yayin zabensa a 2007 ya jagoranci ta’addanci da ya yi sanadin rayuka da dama a jihar.

Ta kuma bukaci Sifetan ‘yan sanda da ya dauki mataki mai tsauri kan wadanda ake zargi da hannu a cikin rikicin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.