Gwamnatin Malam Dikko Ta Bankaɗo Wasu Illoli da Ƴan Bindiga Suka Yi Wa Jama'a a Katsina

Gwamnatin Malam Dikko Ta Bankaɗo Wasu Illoli da Ƴan Bindiga Suka Yi Wa Jama'a a Katsina

  • Gwamnatin jihar Katsina ta bayyana wasu daga cikin illolin da matsalar tsaro ta haifar a rayuwar al'ummar jihar
  • Ta ce sama da makarantu 120 aka rufe yayin da asibitioci 58 suka daina aiki a faɗin jihar duk sanadin ayyukan ta'addanci
  • Gwamna Malam Dikko Raɗɗa ya kaddamar da kwamitin ƙungiyar Imo da zai yi aikin sasanta rikici a Arewa maso Yamma

Jihar Katsina - Akalla makarantu 123 ne aka ce an rufe su gaba daya a jihar Katsina sakamakon ayyukan ‘yan bindiga da sauran miyagun da ke addabar al’ummar jihar.

Gwamnan Katsina, Malam Dikko Radda.
An Kulle Makarantu Sama da 120, Asibitoci 58 Sun Daina Aiki, Gwamnatin Katsina Hoto: @Miqdad_jnr
Asali: Twitter

Haka nan kuma gwamnatin jihar ta bayyana cewa akalla cibiyoyin kiwon lafiya 58 ne suka daina aiki kwata-kwata sakamakon matsalar rashin tsaro, Channels TV ta ruwaito.

Mai ba Gwamna Dikko Radda shawara na musamman kan wadanda rikicin ‘yan bindiga ya shafa da ‘yan gudun hijira, Sa’idu Ibrahim Danja ne ya bayyana hakan ranar Alhamis a Katsina.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP da kujerarsa ke tangal-tangal ya nemi afuwar talakawan jiharsa kan abu 1 da ya faru

Hadimin gwamnan ya yi wannan jawabi ne a wurin kaddamar kwamitin magance rikice-rikice da sulhunta al'umma na ƙungiyar IMO ta duniya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake jawabi ga kwamitin wanda zai yi aiki a Arewa maso Yamma, hadimin gwamnan ya ce:

"Idan kuka sasanta bangarorin biyu da ke rikici, tilas ku duba me zaku iya yi don inganta rayuwarsu, manoma sun yi asarar komai, makiyaya sun rasa shanunsu da muhallinsu.
"Muna da wakilai da hakimai a matakan kananan hukumomi, idan muka haɗa kai aikinmu zai zo da sauki. Mu cire son rai zai taimaka wajen kawo ƙarshen matsalar ƴan gudun hijira."

Gwamna Raɗda ya kaddamar da kwamitin

Bayan haka ne Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Radda ya kaddamar da kwamitin a hukumance.

Gwamnan wanda mataimakin shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin Katsina, Mukhtar Saulawa ya wakilta, ya yi maraba da tallafin ƙungiyar IOM.

Kara karanta wannan

Wike vs Fubara: Jerin gwamnonin da suka yi nasara kan iyayen gidansu na siyasa

“Duk da cewa rikice-rikice da jayayya wani bangare ne na rayuwar dan Adam, abu mafi muhimmanci shi ne yadda za a warware rikici ta hanyar maslaha."
"Muna da hanyoyin gargajiya na magance rikice-rikice waɗanda har yanzu suna da amfani a yau. Sun hada da sasantawa, sulhu, da tattaunawa,” in ji shi.

Sojoji sun ceto ƴan bautar ƙasa NYSC

A wani rahoton kuma Dakarun soji da taimakon 'yan sanda sun samu nasarar ceto 'yan bautar ƙasa biyu daga hannun ƴan bindiga a jihar Katsina.

Kakakin hukumar sojin Najeriya, Onyema Nwachukwu, ya ce ƴan bindiga sun sace mambobin NYSC ne a hanyar zuwa Katsina daga Edo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262