Wike vs Fubara: Jerin Gwamnonin da Suka Yi Nasara Kan Iyayen Gidansu Na Siyasa

Wike vs Fubara: Jerin Gwamnonin da Suka Yi Nasara Kan Iyayen Gidansu Na Siyasa

Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara, ya zama na baya-bayan nan a irinsa da ya samu saɓani da ubangidansa a siyasance, Nyesom Wike, ministan babban birnin tarayya Abuja, amma har yanzu ba a kai ga kawo ƙarshen ɓarakar su ba, ba a kuma yi hasashen kawo karshen rikicin nasu ba domin har yanzu suna takun saƙa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum da nishaɗi

Yayin da Fubara yake samun goyon baya daga kafafen sada zumunta, dattawan jihar sun nuna goyon bayansu ga Wike tare da tunatar da gwamnan yadda ministan ya samar da shi da sauran masu riƙe da muƙaman gwamnati a jihar.

Wike da Fubara sun samu sabani
Fubara da sauran gwamnonin da suka samu sabani da iyayen gidansu na siyasa Hoto: Nyesom Wike
Asali: Twitter

To sai dai kuma a fagen siyasar Najeriya wasu gwamnonin da ke kan karagar mulki sun yi faɗa da iyayen gidansu kuma sun samu nasara a kansu. Ga jerinsu a nan ƙasa:

Kara karanta wannan

Gwamnatin Malam Dikko ta bankaɗo wasu illoli da ƴan bindiga suka yi a Jihar Katsina

Chimaroke Nnamani da Sullivan Chime

Tsofaffin gwamnonin jihar Enugu guda biyu sun kasance ubangidan siyasa da yaronsa, kafin daga bisani Chime ya raba gari da Nnamani.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Chime ya samu nasara a fafatawar sa ta siyasa da magabacinsa Nnamani inda ya mulki jihar na tsawon shekara takwas.

Adams Oshiomhole da Godwin Obaseki

A jihar Edo dai Gwamna Obaseki da magabacin sa sun samu saɓani gabanin sake zaɓen gwamnan.

Rashin jituwa tsakanin Obaseki da Oshiomhole ne yasa gwamnan ya bar jam'iyyar All Progressives Congress (APC) zuwa jam'iyyar PDP.

Oshiomhole dai ya yi wa mataimakinsa Pius Odubu karan tsaye, wanda ya so ya yi takarar gwamna, daga bisani kuma ya goyi bayan Obaseki. Har yanzu Oshiomhole da Obaseki ba su sasanta rikicin da ke tsakaninsu ba.

Orji Kalu da Theodore Orji

Irin wannan dambarwar ta faru a siyasar Abia lokacin da Orji Kalu ya tabbatar da nasarar Theodore Orji a matsayin gwamnan jihar, duk da yana gidan yari.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga da yawa sun mutu yayin da sojoji suka kai samame wasu yankuna a jihar Kaduna

Sai dai, an samu saɓani tsakaninsa da yaronsa na siyasa. Su biyun har yanzu ba su sasanta ba, kuma a wasu lokuta suna takalar juna a kafafen yaɗa labarai.

Rabiu Kwankwaso da Abdullahi Ganduje

Tarihi ya nuna cewa tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje, ya kasance mai cin gajiyar tafiyar Kwankwasiyya ta Rabiu Kwankwaso, wanda ya gabace shi amma ba da dadewa ba su biyun suka rabu saboda saɓanin siyasa.

Rikicin da ke tsakanin Kwankwaso da Ganduje ya sake kunno kai a zaɓen 2023 lokacin da shugaban jam'iyyar APC na ƙasa a yanzu ya taka kafarsa a kan hoton da ke dauke da hoton tsohon ubangidansa na siyasa.

Abubuwan da Suka Haddasa Rigima Tsakanin Wike, Fubara

A wani labarin kuma, kun ji cewa akwai wasu manyan abubuwa guda biyu da suka haddasa rikici a tsakanin Wike da Gwamna Fubara.

Rahotanni sun yi nuni da cewa daga cikin abubuwan da suka haddasa rikici a tsakaninsu har da, naɗa sabbin kwamishinoni da Fubara ya yi ba tare da sanin Wike ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng