'Yan Bindiga da Yawa Sun Mutu Yayin da Sojoji Suka Kai Samame Wasu Garuruwa a Kaduna
- Sojoji sun samu nasarar halaka ƴan bindiga bakwai a kananan hukumomin Chikun da Birnin Gwari a jihar Kaduna
- Rundunar sojin ta kuma bayyana cewa sun kwato muggan makamai daga hannun ƴan bindigan a samamen da suka kai
- Wannan na zuwa ne yayin da lamarin tsaro ke ƙara taɓarbarewa musamman a yankin Birnin Gwari
Ahmad Yusuf, gogaggen Edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa da al'amuran yau da kullum
Jihar Kaduna - Dakarun sojojin rundunar Operation Whirl Punch sun halaka ƴan bindiga bakwai yayin da suka kai samamen shara a kanan hukumomi biyu na jihar Kaduna.
Kamar yadda Channels tv ta ruwaito, Sojojin sun samu nasarar raba ƴan ta'addan da duniya a Birnin Gwari da Chikun duk a jihar da ke Arewa maso Yamma.
Sojoji zasu yi juyin mulki a Najeriya? Babban hafsan tsaro CDS Musa ya yi bayanin da ya kamata ku sani
Mataimakin daraktan yaɗa labarai na rundunar, Laftanar Kanal Musa Yahaya, shi ne ya tabbatar da wannan nasara ranar Jumu'a, 3 ga watan Nuwamba, 2023.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda sojojin suka samu nasara
Ya bayyana cewa sojojin sun yi nasarar kashe wasu ‘yan bindiga hudu da suka addabi mazauna kauyen Kampanin Doka da ke Birnin Gwari a yayin farmakin.
Haka nan kuma sun kwato muggan makamai da kayan aiki da suka haɗa da bindiga ƙirar AK-47 guda daya, magazine da kuma babura 14 daga hannun barayin.
A wani samame da sojojin suka kai, sun kashe dan bindiga a yayin da suka yi yunkurin kai wa wasu manoma hari a kauyen Sabon Sara, sauran suka gudu ɗauke da raunuka.
A yayin samamen sojojin sun kwato bindigu kirar AK-47 guda biyu, sai kuma daya daga cikin manoman mai suna Abdulrahman Aliyu ya samu raunuka.
Kakakin rundunar ya kara da cewa dakarun sun kashe ‘yan bindiga biyu a wani farmaki da suka kai yankunan Kankomi, Juji, Gwantu, Kujeni, Kikwari da Kaso a karamar hukumar Chikun.
Ya kuma bayyana cewa sojojin sun kwato wasu muggan makamai da suka hada da bindiga kirar AK-47 da alburusai daga hannun ‘yan fashin dajin, Vanguard ta ruwaito.
Sojoji sun kwato yan bautar kasa a Katsina
A wani rahoton kuma Dakarun soji da taimakon 'yan sanda sun samu nasarar ceto 'yan bautar ƙasa biyu daga hannun ƴan bindiga a jihar Katsina.
Kakakin hukumar sojin Najeriya, Onyema Nwachukwu, ya ce ƴan bindiga sun sace mambobin NYSC ne a hanyar zuwa Katsina daga Edo.
Asali: Legit.ng