Lawal da Ndume: Kotun Daukaka Kara Ta Yanke Hukunci Kan Nasarar Sanatocin APC Biyu

Lawal da Ndume: Kotun Daukaka Kara Ta Yanke Hukunci Kan Nasarar Sanatocin APC Biyu

  • Kotun ɗaukaka ƙara ta raba gaddama kan sahihancin zaɓen Sanatocin jam'iyyar APC biyu daga jihar Borno
  • A zaman yanke hukunci, kwamitin alƙalan Kotun ya kori karar da aka ƙalubalanci Ali Ndume da Kaka Lawal bisa rashin cancanta
  • INEC ta ayyana Ndume da Lawal a matsayin waɗanda suka ci zaɓen Borno ta kudu da Borno ta tsakiya a zaɓen watan Fabrairu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, gogaggen Edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Kotun ɗaukaka ƙara mai zama a Abuja ta yanke hukuncin ƙarshe kan nasarar Sanatoci biyu da suka fito daga jihar Borno a Arewa maso Gabas.

A rahoton The Nation, Kotun ta tabbatar da nasarar Sanata Muhammed Ali Ndume (Borno ta kudu) da Sanata Kaka Lawal (Borno ta tsakiya) a zaɓen da ya gabata.

Kara karanta wannan

Kotun ɗaukaka ƙara ta ƙwace kujerar ɗan majalisar tarayya na PDP, ta bada sabon umarni

Sanata Muhammed Ali Ndume.
Lawal da Ndume: Kotun Daukaka Kara Ta Yanke Hukunci Kan Nasarar Sanatocin APC Biyu Hoto: Ali Ndume
Asali: UGC

Kwamitin alƙalai uku na Kotun karkashin jagorancin mai shari’a Biobele Georgewill, ya bayyana cewa kararrakin biyu da aka ƙalubalanci ‘yan majalisar ba su cancanta ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hukumar dillancin labarai (NAN) ta rahoto cewa hukumar zaɓe INEC ta ayyama Ndume da Lawan a matsayin waɗanda suka samu nasara a zaɓen mazaɓun biyu.

Idan baku manta ba a ranar 25 ga watan Fabrairun 2023 aka yi zaɓen shugaban ƙasa, Sanatoci da ƴan majalisar wakilan tarayya.

Kotun zaɓe ta yi hukunci

Bisa rashin gamsuwa da wannan sakamkon da INEC ta bayyana, Muhammed Kumalia na PDP ya garzaya Kotun zaɓe ya kalubalanci nasarar sanata Lawal.

Haka a ɗaya ɓangaren, Kudla Satumari da jam'iyyar PDP suka durfafi Kotu, inda suka kalubalanci nasarar Ali Ndume, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Sai dai bayan sauraron kowane ɓangare, Kotun sauraron ƙararrakin zaben ƴan majalisar jiha da na tarayya ta kori kararrakin biyu yayin yanke hukunci.

Kara karanta wannan

Kotu ta kwace kujerar sanatan PDP, ta tabbatar da dan takarar APC a matsayin wanda ya lashe zabe

Abin da ya faru a Kotun ɗaukaka ƙara

Duk da haka ƴan takarar jam'iyyar adawan biyu suka ƙi haƙura, suka sake shigar da ƙara a Kotun ɗaukaƙa ƙara mai zama a Abuja.

Amma da take take yanke hukunci, Kotun ɗaukaka ƙarar ta yi fatali da ƙararrakin biyu bisa rashin cancanta, sannan ta tabbatar da nasarar Ndume da Lawal.

An kwace nasarar ɗan majalisar PDP

A wani rahoton na daban Kotun ɗaukaka ƙara ta tabbatar da hukuncin ƙaramar Kotu wanda ya ayyana zaben ɗan majalisar Birnin Kudu/Buji a matsayin wanda bai kammalu ba.

A zaman yanke hukunci, Kotun ta umarci hukumar zaɓe ta ƙasa.INEC ta shirya sabon zaɓe a rumfuna 8 cikin kwanaki 30.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262