Kotu Ta Shiga Tsakani, Ta Yanke Hukunci Kan Yunkurin Tsige Gwamnan PDP
- Babbar kotun Ribas ta raba gardama a shari'ar Gwamna Simi Fubara da majalisar dokokin jihar
- Mai shari’a Ben Whyte ya dakatar da yunkurin da majalisar ke yi na tsige gwamnan jihar daga kujerarsa
- Kotun ta dage zaman zuwa ranar 14 ga Nuwamba, 2023 domin ci gaba da sauraron shari'ar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Jihar Rivers - Wata babbar kotun Ribas da ke yankin Isiokpo a karamar hukumar Ikwerre ta jihar ta ba da umurnin wucin gadi na hana majalisar dokokin jihar Ribas da kakakin majalisar, Martin Amaewhule tsige gwamnan jihar, Siminalayi Fubara.
Alkalin kotun, mai shari’a Ben Whyte ya bayar da umarnin ne bayan karar da aka shigar a kan wadanda ake kara.
Kotu ta hana majalisar Ribas tsige Fubara
Whyte ya ba da umarnin cewa bangarorin su ci gaba a yadda ake har zuwa lokacin da za a yanke hukunci kan bukatar da aka gabatar sannan kuma ya dage zaman zuwa ranar 14 ga Nuwamba, 2023, Channels TV ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jaridar Punch ma ta ba da rahoto a kan ci gaban.
Umurnin kotun na cewa:
“Saboda haka an yi umarnin cewa bangarorin da ke cikin shari’ar su ci gaba da kasancewa a halin da ake ciki a shari’ar da mai kara a matsayin Gwamnan Jihar Ribas ya shigar har zuwa lokacin da za a gabatar da bukatar da ake magana a kai.
"An dage sauraron karar zuwa ranar 14 ga watan Nuwamba, 2023 domin fafatawa a kan karar da aka shigar."
Wike ya bayyana zunuban Fubara
A gefe guda, mun ji cewa tsohon gwamnan jihar Ribas kuma ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, ya bayyana dalilan da suka haddasa rigima tsakaninsa da magajinsa kuma tsohon na hannun damarsa, Siminalayi Fubara.
Bayan ganawa da wasu gwamnonin PDP a Abuja a ranar Laraba, 1 ga watan Nuwamba, Mista Wike ya zargi Fubara da hulda da abokan hamayyarsa na siyasa, kamar yadda PremiumTimes ta rahoto.
"Ba za ka yi aiki ba, sannan mutane su fara kawo makiyanka; wadanda suka yake ka lokacin da kake fadi tashi don mutumin ya hau karagar mulki. Babu mai yin haka", Kamfanin dillancin labaran Najeriya ta nakalto ministan yana fadi.
Asali: Legit.ng