Bode George Na Shirin Barin Najeriya Bayan Kotun Koli Ta Tabbatar da Tinubu? Jigon PDP Ya Magantu

Bode George Na Shirin Barin Najeriya Bayan Kotun Koli Ta Tabbatar da Tinubu? Jigon PDP Ya Magantu

  • Cif Bode George, jigon jam'iyyar PDP, ya yi karin haske cewa ba ya niyar barin kasar bayan nasarar da Shugaba Bola Tinubu ya samu a zaben shugaban kasa a 2023
  • A baya George ya bayyana cewa zai bar Najeriya idan Tinubu ya yi nasara, amma yanzu ya yi bayanin cewa zaurance ya yi
  • Tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar PDP na kasa ya kuma yi magana kan yiwuwar sulhu da gwamnatin Tinubu

Jihar Lagos - Cif Bode George, jigon jam'iyyar PDP, ya yi watsi da duk wani shiri na yin kaura daga kasar bayan kotun koli ta tabbatar da nasarar shugaban kasa Bola Tinubu, Daily Trust ta rahoto.

Tsohon mataimakin shugaban na jam'iyyar PDP na kasa ya sha alwashin barin Najeriya idan Tinubu ya lashe zaben shugaban kasa na 2023.

Kara karanta wannan

Peter Obi Ya Shiga Yar Buya Bayan Ya Sha Kaye a Kotun Koli? Kakakin Kamfen Din LP Tanko Ya Magantu

Bode George ya ce ba zai bar Najeriya ba bayan nasarar Tinubu
Bode George Na Shirin Barin Najeriya Bayan Kotun Koli Ta Tabbatar da Tinubu? Jigon PDP Ya Magantu Hoto: @naomi_onome, @PBATMediaCentre
Asali: Twitter

A karshe Tinubu ya lashe zaben shugaban kasar na ranar 25 ga watan Fabrairu. Duk kokarin da yan adawa suka yi na ganin an tsige shi ya ci tura inda kotun koli ta tabbatar da nasararsa a ranar Alhamis, 26 ga watan Oktoba.

Na yi magana da zaurance ne, Inji Bode George

A wata hira da Daily Trust, George ya ce bai da niyar barin Najeriya duk da nasarar da Tinubu ya yi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jigon na PDP ya ce:

"Ina magana da zaurance ne. Wannan zai zama shekara ta 25 da na shiga siyasa. Na kuma shafe shekaru 25 a rundunar sojoji.
"Yanzu ina tunkarar shekaru 80 a duniya, don haka me nake nema da ya wuce na je na yi rayuwa a inda zan iya tafiya ba tare da na duba gaba da baya don ganin wa ke bibiya na ba, wurin da zan iya samun kwanciyar hankali har sai Allah madaukakin sarki ya kirani."

Kara karanta wannan

Kotun Koli: Jam’iyyar LP Ta Taya Tinubu Murna, Ta Aika Sako Ga Atiku

Bode George ya magantu kan sulhu da Tinubu

Da aka tambaye shi ko akwai yiwuwar yin sulhu tsakaninsa da gwamnatin Tinubu, George ya ce:

"Abun ban sha'awa shine cewa abokina ne shi; addu'ar da ya yi mini ke nan. Na yi aiki tare da shugabannin kasa biyar a kasar nan, don haka bana bukatar kowani aiki daga wajen kowa."

Bode George ya magantu kan zaben 2023

A wani labarin, mun ji a baya cewa tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar PDP na ƙasa, Cif Bode George, ya yi tsokaci kan rawar da kotunan Najeriya ke takawa wajen tabbatar da ɗan takarar da ya yi nasara a zaɓe.

Ya yi kira ga kotun zaɓe da ta yi ƙoƙarin yin adalci wajen yanke hukunci ta hanyar bai wa mutane ainihin abinda suka zaɓa kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng