'Yan Siyasa 5 Masu Neman Shugaban Kasa da Tinubu Ya Bai Wa Mukami a Gwamnatinsa

'Yan Siyasa 5 Masu Neman Shugaban Kasa da Tinubu Ya Bai Wa Mukami a Gwamnatinsa

  • Wasu daga cikin fitattun ‘yan siyasar sun shiga zaben tsaida gwani da nufin samun mulkin Najeriya a zaben 2023
  • A karshe Bola Ahmed Tinubu ya yi nasara kuma ya jawo su a gwamnatinsa, ya ba su mukamin Minista ko wata kujerar
  • Fela Durotaye wanda ya yi takara da Muhammadu Buhari a AAN ya cikin jerin masu taimakawa gwamnatin Tinubu

Abuja - Daga jam’iyyu da-dama, mutane da yawa su ka nemi samun tikiti domin tsayawa takarar shugaban kasar Najeriya da aka yi a bana.

A rahoton nan, mun kawo jerin wadanda su ka yi harin kujerar nan, amma a karshe sai ga shi Bola Tinubu ya ba su mukami a gwamnatinsa.

Tinubu
'Yan takaran da Bola Tinubu ya ba mukami Hoto: TopChrisBoy, David Umahi
Asali: Twitter

1. Nyesom Wike

Nyesom Wike ya shiga zaben gwani a PDP domin ya yi takarar shugaban kasa, yayin da Atiku Abubakar ya doke shi sai ya yaki ‘dan takaran jam’iyyarsa.

Kara karanta wannan

Albishir da Tinubu Ya Yi wa Hadimai Jim Kadan da ba Shi Nasara a Shari’ar Zaben 2023

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A dalilin goyon bayan Bola Tinubu wasu su ka nemi korar Ministan na Abuja daga PDP.

2. Muhammad Badaru

Da farko Muhammad Badaru ya nemi tikitin jam’iyyar APC a zaben shugaban kasa, daga baya ya janye saboda a bar mulki ya koma yankin kudancin Najeriya.

Bayan lashe zabe sai sabon shugaban kasa ya nada shi a matsayin ministan harkar tsaro.

3. David Umahi

Kamar Badaru, a lokacin shi ma ya na Gwamna, David Umahi ya yi yunkurin zama ‘dan takaran APC a zaben shugaban kasa, shi ma bai iya samun tikiti ba.

A lokacin ya na Sanata, aka aika fitar da sunansa a ministoci, ya na rike da ma’aikatar ayyuka.

4. Uju Kennedy-Ohanenye

Barista Uju Kennedy-Ohanenye ta yi sha’awar zama ‘yar takarar APC ta shugaban kasa a zaben 2023, kafin zabe ta sanar da cewa ta janyewa Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

Kotun Koli: Babban Mai Adawa Da Buhari Ya Taya Tinubu Murna, Ya Aika Gagarumin Sako Ga Atiku

Yanzu haka ta zama Ministar harkokin mata, an ba ta mukami kamar yadda ta roka.

5. Fela Durotaye

Shi Fela Durotaye ya tsaya takarar shugabancin kasar nan ne a zaben 2019 a karkashin jam’iyyar AAN ya kuma samu goyon bayan kananun ‘yan takara 11.

Shekaru hudu bayan ya sha kashi a hannun APC, Durotaye ya samu mukami a Aso Rock.

Rarara ya soki Gwamnatin Buhari

Ana da labari Dauda Adamu Kahutu da aka fi sani da Rarara ya fito ya na sukar Muhammadu Buhari bayan nasarar Bola Tinubu a kotun koli.

Bashir Ahmaad wanda ya yi aiki da tsohon shugaban Najeriyan ya aika masa martani a Facebook, ya ce hankali ba zai dauki maganganun ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng