Fela Durotoye ya dauko Khadija Iya tayi masa mataimakiya a 2019
- Fela ya zabi Khadija a matsayin mataimakiyar sa
- Mataimakiyar shugaban kasa zata kasance mace
- Ina farin cikin bayyana muku Khadija a matsayin mataimaki ya ta
Dan takarar neman kujerar shugaban kasa a jam'iyar ANN Fela Durotoye ya zabi Hajia Khadija Abdullahi Iya a matsayin matamakiyar sa a zaben shekara ta 2019.
A ranar Laraba Durotoye ya bayyana cewa "ina farin cikin bayyana muku mataimakiya ta sannan da goyan bayan ku insha Allah Khadija itace zata kasance mataimakiyar shugaban kasa anan gaba."
Hajiya Khadija Abdullahi-Iya, ita ce 'yar arewa ta biyu da wani dan takara daga kudu ya dauko don zama mataimakiyarsa, ta farko ita ce Hajiya Getso mai shekaru 37 daga jihar Kano, wadda Moghalu na YPP ya zabo a makon nan shima.
DUBA WANNAN: Me sabon littafin tsohon shugaba Jonathan da aka gabatar jiya ya qunsa?
Khadija na da shaidar kamma digiri da mastas a bangaren Shari'a wanda tayi a jami'ar Abuja.
Kasantuwar Khadija akan wannan mukami zai taimaka kwarai a bangaren ilimi tunda ita jajirtacciya ce a wannan fage.
Ta karbi lambar yabo akan jajircewar ta wajen bunkasar ilimi baya ga sana'o'i da ta samar.
Khadija dai matace a wajen tsohon difuti ciyaman na bankin kasa CBN Alhaji Haruna Dalhatu Iya.
Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng
Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng