“Za a Yi Rawan Murna Ta Ko’ina”: LP Ta Sha Alwashi Gabannin Hukuncin Kotun Koli

“Za a Yi Rawan Murna Ta Ko’ina”: LP Ta Sha Alwashi Gabannin Hukuncin Kotun Koli

  • Kotun koli, wacce ita ce kankat, za ta zartar da hukunci kan takkadamar zaben shugaban kasa a ranar Alhamis, 26 ga watan Oktoba
  • Manyan jam'iyyun adawar kasar sun ce an yi magudi a sakamakon zaben na watan Fabrairun 2023 da hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta fitar
  • Kasa da awanni 24 kafin rufe shari'ar da jam'iyyun adawa suka shigar kotun koli, jam'iyyar LP, wacce ta zo na uku a zaben, ta ce tana da yakinin yin nasara a kotu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

FCT, Abuja - Jam'iyyar LP ta ce tana da yakinin yin nasara a kotun koli a ranar Alhamis, 26 ga watan Oktoba.

Kamar yadda jaridar Vanguard ta rahoto, jam'iyyar ta bayyana hakan ne a ranar Laraba, 25 ga watan Oktoba, ta bakin lauyanta, Kehinde Edun.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC Ta Yi Martani Bayan INEC Ta Cire Sunan Dan Takararta a Cikin Jerin Yan Takarar Gwamnan Bayelsa

Jam'iyyar LP ta ce za ta yi nasara a kotun koli
“Za a Yi Rawan Murna Ta Ko’ina”: LP Ta Sha Alwashi Gabannin Hukuncin Kotun Koli Hoto: Senator Athan Nneji Achonu
Asali: Facebook

Peter Obi, tsohon gwamnan jihar Anambra, shine dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar.

Da yake magana gabannin ranar yanke hukuncin, jaridar The Nation ta nakalto Edun yana cewa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Muna tsammanin nasara saboda shine abun da adalci yake bukata; abin da yan Najeriya suke so kenan, ba za mu yanke kauna ba, mun gabatar da kararmu a gaban kotu.
“Muna da yakinin jam’iyyar LP da yan Najeriya za su samu nasara. Mun san cewa za a yi tsallen murna a ko’ina a Najeriya.”

Kotun koli za ta yanke hukuci a shari'ar Tinubu

A baya mun ji cewa kotun koli ta tsaida gobe a matsayin ranar da za ta yanke hukunci a kan karar zaben shugaban kasar Najeriya na 2023.

A safiyar yau rahoto ya fito daga Punch cewa kotun koli za ta zauna domin yanke hukuncin karshe a shari’ar zaben shugaban Najeriya.

Kara karanta wannan

Yanzu Nan: Kotun Koli Ta Fadi Ranar Yanke Hukunci a Karar Tinubu v Atiku da Obi

Jigon PDP na so ayi waje da Tinubu

A wani labarin, wani jigo jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Abdul-Aziz Na’ibi Abubakar, ya buƙaci kotun ƙoli ta kori shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.

Ya ce ya kamata kotun ƙoli ta bayyana ɗan takarar PDP, Atiku Abubakar a matsayin shugaban Najeriya.

Abubakar, wanda shi ne Darakta Janar na yada labarai na kungiyar Atiku The Light, ya ce korar da kotun koli za ta yi wa Tinubu, za ta ceci Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel