Gwamnonin APC Na Kudu Maso Yamma Sun Gana Da Seyi Makinde
- Gwamna Seyi Makinde ya karɓi baƙuncin wasu gwamnoni a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar APC a birnin Ibadan, a ranar Talata, 24 ga watan Oktoba
- Gwamnan na PDP ya yi wata ƴar gajeruwar ganawa da gwamnonin, Babajide Sanwo-Olu (Lagos), Dapo Abiodun (Ogun), da Biodun Oyebanji (Ekiti) a ofishinsa da ke Ibadan
- Ba a samu cikakken bayanai kan ganawar tasu ba amma dai gwamnonin na APC sun je jihar ne domin duba takwaransu na jihar Ondo, Rotimi Akeredolu a gidansa da ke Ibadan
Ibadan, jihar Oyo - Gwamnonin jihohin Kudu maso Yamma a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar APC mai mulki sun kai ziyara a birnin Ibadan, babban birnin jihar Oyo a ranar Talata, 24 ga watan Oktoban 2023.
Gwamnonin da suka haɗa da Babajide Sanwo-olu (Lagos), Dapo Abiodun (Ogun), da Biodun Oyebanji (Ekiti) sun samu tarba a ranar Talata a wajen takwaransu na jihar Oyo, Seyi Makinde.
Kamar yadda rahoton jaridar The Nation ya tabbatar, gwamnonin waɗanda suka isa daban-daban a sakatariyar gwamnatin jihar Oyo, dake Agodi a Ibadan, sun samu tarba daga mai masaukin baƙi, gwamna Makinde a ofishinsa.
Sanwo-Olu, wanda ya zo na ƙarshe a cikin jirgin sama mai saukar ungulu, daga baya ya haɗu da takwarorinsa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Meyasa gwamnonin suka gana da Makinde?
Gwamnonin dai sun isa jihar Oyo ne domin duba takwaransu na jihar Ondo, gwamna Rotimi Akeredolu, wanda yake fama da rashin lafiya.
Sai dai, gwamnonin huɗu sun yi wata ƴar gajeruwar ganawar sirri a ofishin gwamnan jihar Oyo kafin su fice daga baya.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ba a bayyana manufar ganawar gwamnonin ba baya ga ziyarar duba gwamna Akeredolu, ko kuma abin da suka tattauna a ganawar ta su.
Gwamnoni Kudu Maso Yamma Sun Ziyarci Akeredolu
A wani labarin kuma, gwamonin jihohin yankin Kudu maso Yamma sun ziyarci takwaransu na jihar Ondo, gwamna Rotimi Akeredolu, a gidansa da ke birnin Ibadan na jihar Oyo.
Gwamnonin waɗanda suka haɗa da Sanwo-Olu, Seyi Makinde, Dapo Abiodun, Biodun Oyebanji sun ziyarci gwamnan ne domin duba lafiyarsa, yayin da yake cigaba da murmurewa daga jinyar da ya dawo ƙasar waje.
Asali: Legit.ng