Zaben Kogi: Tsohon Mataimakin Gwamna Ya Fice Daga Jam'iyyar PDP

Zaben Kogi: Tsohon Mataimakin Gwamna Ya Fice Daga Jam'iyyar PDP

  • Rikicin jam'iyyar PDP a Kogi ya ɗauki sabon salo yayin da tsohon mataimakin gwamna ya fice daga jam'iyyar a hukumance
  • Arc Abayomi Awoniyi, ya aike da takardar murabus dinsa daga PDP zuwa ga shugaban jam'iyyar na ƙaramar hukumar Mopamuro
  • Alamu masu ƙarfi sun nuna cewa jigon siyasar na shirin sauya sheka zuwa APC mai mulki nan bada daɗewa ba

Kogi - Rikicin da ya ɓarke a jam'iyyar PDP reshen jihar Kogi ya buɗe sabon shafi jiya Alhamis, 7 ga watan Satumba, 2023.

Tsohon mataimakin gwamnan jihar Kogi a inuwar jam'iyyar PDP, Arc Abayomi Awoniyi, ya fice daga jam'iyyar a hukumance.

Tsohon mataimakin gwamnan jihar Kogi, Arc Abayomi Awoniyi.
Zaben Kogi: Tsohon Mataimakin Gwamna Ya Fice Daga Jam'iyyar PDP Hoto: Leadership
Asali: UGC

Ya ce zai fice daga jam’iyyar ne bayan shafe shekaru 25 na aminci da sadaukar da kai da hidimtawa PDP, kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito.

Kara karanta wannan

To Fa: Atiku Abubakar Ya Shiga Sabuwar Rigima Yayin da Yake Shirin Ɗaukaka Kara Zuwa Kotun Ƙoli

Awoniyi wanda ya rike mukamin mataimakin tsohon Gwamna Idris Wada, ya mika takardar murabus din sa ne ga shugaban jam’iyyar PDP a karamar hukumar Mopamuro ta jihar Kogi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai bai bayyana wace jam'iyya zai koma ba a cikin wasiƙar, wacce ke ɗauke da kwanan watan 31 ga watan Agusta, 2023.

Duk da bai ambaci dalilinsa na barin jam'iyyar PDP ba amma ana tsammanin ficewarsa ba zata rasa nasaba da rashin gamsuwa da zaɓen fidda gwanin takarar gwamna ba.

Wace jam'iyya tsohon mataimakin gwamna zai koma?

Alamu masu ƙarfi sun nuna cewa tsohon mataimakin gwamnan na shirye-shiryen sauya sheka zuwa jam'iyyar APC mai mulki nan ba da daɗewa ba.

Ya yi wa takardar take da, “Wasikar murabus daga jam’iyyar PDP” kuma ta shiga hannun manema labarai ne jiya Alhamis.

Kara karanta wannan

Bayan Korar Kwankwaso, Tsohon Shugaban NNPP Na Ƙasa Ya Fice Daga Jam'iyyar Kan Abu 1

Vanguard ta rahoto wani sashin wasiƙar na cewa:

"Na rubuta wannan takarda ne domin sanar da murabus ɗina daga jam'iyyar PDP bayan kwashe shekaru 25 ina biyayya, sadaukarwa da hidima."
"Ina mika sakon godiyata ga duka 'ya'yan PDP a karamar hukumar Mopamuro da ke Kogi ta Yamma, da ɗaukacin jihar baki daya bisa goyon bayan da suka bani da hadin kai tsawon shekaru."

Shugaba Tinubu Ya Bayyana Tarihin Karatunsa a Jami'a

A wani rahoton na daban kuma Shugaba Bola Tinubu ya bayyana tarihinsa na karatu a lokacin da yake jami'a, inda ya ce shi hazikin dalibi ne.

Yayin da yake jawabi ga ‘yan Najeriya mazauna Indiya, shugaban ya faɗi yadda Deloitte ya horar da shi sannan ya shiga kamfanin Exxon Mobil.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262