Kotu Ta Bayyana Kujerar Sakataren Jam'iyyar PDP Na Kasa a Matsayin Wacce Ba Kowa a Kanta
- Kotu ta bayyana kujerar Samuel Anyanwu, ɗan takarar gwamna a jam'iyyar PDP a jihar Imo, ta sakataren jam'iyyar PDP na ƙasa a matsayin wacce ba kowa a kanta
- Kotun wacce ke zamanta a Enugu ta bayar da umarnin ne a ƙarar da Nwabueze Ugwu ya shigar na a yarda da wanda ya maye gurbin Anyanwu, Sunday Udeh-Okoye
- Kotun ta tilasta wa wadanda ake ƙara da su amince da wannan umarni har sai lokacin da ta yanke hukunci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Enugu, jihar Enugu - Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Enugu ta bayyana kujerar ofishin sakataren jam'iyyar PDP na ƙasa a matsayin wacce ba kowa a kanta.
Kotun ta bayyana hakan ne a ƙarar da Nwabueze Ugwu ya shigar a gabanta, cewar rahotom TVC.
A wani umarni na wucin gadi, kotun ta tilasta wa wadanda ake ƙara a ƙarar da suka haɗa da shugaban jam'iyyar PDP na ƙasa, sakataren jam'iyyar na ƙasa da su amince da Sunday Udeh-Okoye, wanda kwamitin zartarwa na shiyyar Kudu maso Gabas, ya kawo ya maye gurbin Anyanwu.
Daga nan ne kotun ta yanke hukuncin cewa Sunday UDEH-Okoye ya maye gurbin Samuel Anyanwu har sai lokacin da ta yanke hukunci kan ƙarar, rahoton The Guardian ya tabbatar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Meyasa kotun ta ƙwace kujerar Anyanwu?
A cewar mai shari’a C.O Ajah, wanda ya shigar da ƙarar ya kawo ƙarar ne a ƙarƙashin sashe na 38 doka ta 1 da sashe na 39 doka ta 1 na dokokin babbar kotun jihar Enugu ta shekarar 2020.
Kotun ta lura cewa ta gamsu da takardu 23 waɗanda mai shigar da ƙarar ya kawo a gabanta.
Sai dai an ɗage ƙarar zuwa ranar 30 ga watan Oktoba domin cigaba da saurarenta.
A kwanakin baya ne masu ruwa da tsaki na jam'iyyar PDP a yankin Kudu maso Gabas a jihar Enugu suka yanke shawarar maye gurbin Samuel Anyanwu, ɗan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a zaben ranar 11 ga watan Nuwamba a jihar Imo.
Masu ruwa da tsakin sun maye gurbin Anyanwu na sakataren jam'iyyar PDP na ƙasa da Sunday UDEH-Okoye a matsayin sabon sakataren jam'iyyar na ƙasa.
PDP Ta Fara Kamfen a Jihar Kogi
A wani labarin kuma, manyan jiga-jigan jam'iyyar PDP sun dira jihar Kogi domin yi wa ɗan takarar gwamnan jam'iyyar, Dino Melaye, kamfen.
Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke da tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki na daga cikin jiga-jigan PDP waɗanda suka dira a jihar Kogi.
Asali: Legit.ng