'Azumi Ya Kamata Kotun Koli Ta Yi Na Kwanaki 3 Don Gano Gaskiyar Takardun Tinubu', Shehu Sani

'Azumi Ya Kamata Kotun Koli Ta Yi Na Kwanaki 3 Don Gano Gaskiyar Takardun Tinubu', Shehu Sani

  • Sanata Shehu Sani ya shawarci kotun koli da ta daukin matakin yin azumin kwanaki uku don gano gaskiyar takardun Tinubu
  • Sanatan ya ce wannan hanya ita ce kadai za ta bayyana musu gaskiyar wasiku ma su cin karo da juna da Jami’ar Chigaco da ba su
  • Sani ya bayyana haka a jiya Litinin 23 ga watan Oktoba a shafinsa na Twitter inda ya ce Najeriya kasa ce da ta yadda da addu’o’i

FCT, Abuja – Tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani ya yi martani kan rudun da aka samu na takardun karatun Tinubu.

A jiya Litinin 23 ga watan Oktoba yayin zaman kotun zaben shugaban kasa, an samu rudani a takardun karatun Shugaba Tinubu.

Shehu ya shawarci kotun koli su yi azumi don gano gaskiyar takardun Tinubu
Shehu Sani ya yi martani kan takardun Tinubu. Hoto: Shehu Sani, Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Meye Shehu Sani ke cewa kan takardun Tinubu?

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu Ya Yi Dabara, Ya Cusa Majalisar Dattawa da Majalisar Wakilai a Aljihu

Kotun ta sanar da cewa akwai rudani a wasikun da Jami’ar Chicago ta tura mata wadda ke cin karo da juna.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da ya ke martani kan wannan rudani, Sanata Shehu Sani ya ce idan har kotun koli ta gagara gano gaskiyar lamarin kan wasikun, ya kamata ta yi azumi.

Sani ya ce abin da yafi kamata shi ne yin azumin kwanaki uku inda ya ce a rana ta karshe, ubangiji zai nuna musu wasikar gaskiya a cikin mafarki.

Wane shawara Sani ya bai wa kotun koli kan takardun Tinubu?

Tsohon sanatan ya bayyana haka ne a shafinsa na Twitter inda ya kara da cewa abu ne mai sauki tun da daman ‘yan Najeriya an sansu da yawan addu’o’i.

Ya ce:

“Idan har kotun koli ta samu wasiku daga Jami’ar Chicago ma su cin karo da juna, abin da ya kamata su yi shi ne azumin kwanaki uku.

Kara karanta wannan

Yajin Aiki Ya Kare: Tinubu Ya Bayyana Ranar Fara Shirin Lamunin Dalibai, Ya Fadi Amfanin Shirin

“A rana ta ukun, ubangiji zai nuna musu na gaskiyar a cikin mafarki, mu na kasa ce da ta yi imani da addu’o’i.”

Wannan na zuwa ne yayin ake ci gaba da sauraran kararrakin zaben shugaban kasa da aka gudanar a watan Faburairu na wannan shekara.

Kotun koli ta yi martani kan takardun Tinubu

A wani labarin, kotun koli ta ce akwai wasiku ma su cin karo da juna da Jami’ar Chicaco ta mika na takardun Tinubu.

Wannan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da sauraran kararrakin zaben shugaban kasa a watan Faburairu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.