PDP Ta Shiga Matsala Yayin da Kotun Daukaka Kara Ta Tsige Sanatan Filato Da Dan Majalisar Wakilai

PDP Ta Shiga Matsala Yayin da Kotun Daukaka Kara Ta Tsige Sanatan Filato Da Dan Majalisar Wakilai

  • Kotun daukaka kara a Abuja ta soke nasarar zaben Simon Mwadkwon a matsayin sanata mai wakiltan Filato ta arewa, saboda gazawar jam’iyyar PDP wajen tsayar da shi
  • Kotun ta yanke cewa PDP bata bi umurnin kotu ba, kasancewar kananan hukumomi 12 basu halarci taron ba
  • Saboda haka, an ba da umarnin sake gudanar da zaben kujerar Sanata mai wakiltan Filato ta Arewa cikin kwanaki 90
  • A halin da ake ciki, wani kwamitin a kotun daukaka karar ya soke nasarar zaben Musa Avia na PDP a majalisar wakilai

FCT, Abuja - Kotun daukaka kara a Abuja, ta soke nasarar zaben Simon Mwadkwon, sanata mai wakiltan Filato ta arewa a majalisar dokokin tarayya.

A hukuncin da ya yanke, kwamitin kotun mai mutum uku karkashin jagorancin Mai shari’a Daudu Williams, ya ce PDP ba ta tsayar da Mwadkwon ba.

Kara karanta wannan

Mista Ibu: Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki Ya Dauki Nauyin Asibitin Jarumin Da Ke Jinya

Kotu ta tsige sanatan PDP
PDP Ta Shiga Matsala Yayin da Kotun Daukaka Kara Ta Tsige Sanatan Filato Da Dan Majalisar Wakilai Hoto: Simon Davou Mwadkwon, Nigerian Senate
Asali: Facebook

Har zuwa lokacin da kotu ta yanke hukuncin, Mwadkwon shi ne shugaban marasa rinjaye na Majalisar Dattawan.

Kamar yadda Channels TV ta rahoto, kotun daukaka karar ta bayyana cewa jam'iyyar PDP bata bi umurnin da kotu ta bata ba kasancewar kananan hukumomi 12 basu halarci taron ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamar yadda kotun ta bayyana, PDP ta ki bin umurnin da babbar kotun jihar Filato ta bayar tun a 2020 na gudanar da taro kafin zaben yan takara.

Filato ta arewa: Kotu ta yi umurnin sake zabe

Bayan soke nasarar Mwadkwon, kotun ta yi umurnin sake sabon zabe kan kujerar sanata mai wakiltan Filato ta arewa cikin kwanaki 90, rahoton The Nation.

A halin da ake ciki, wani kwamitin na kotun daukaka karar karkashin jagorancin Maishari'a Okon Abang ta kuma soke nasarar Musa Avia, dan majalisa mai wakiltan Bassa ta arewa a majalisar wakilai.

Kara karanta wannan

PDP Ta Sake Karbar Kaya Yayin da Kotu Ta Yi Fatali da Korafinta a Zaben Majalisar Tarayya, Ta Bai Wa LP Nasara

Cikakken jerin kararrakin zaben da kotun daukaka kara ta saurara a kwana 9 da suka wuce

A wani labarin, mun kawo cewa kotun daukaka ƙara a Najeriya (CoA) ta saurari wasu ƙararrakin zaɓe da aka yi a makon nan.

Kada ka bari komai ya wuce ka Wannan dai na faruwa ne a daidai lokacin da shugabar kotun daukaka ƙara, mai shari’a Monica Dongban-Mensem, ta umurci jam'iyyun siyasa da lauyoyinsu da su mayar da duk wasu ƙararrakin da suka taso daga ƙararrakin zaɓe a faɗin ƙasar zuwa kotunan ɗaukaka ƙara na Abuja da Legas.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng