Zaben Kogi: Fasto Ikuru Ya Yi Hasashen Nasara Ga Ododo
- Kwanaki 20 a gudanar da zaɓen gwamnan jihar Kogi na 2023, Fasto kuma jigo a jam’iyyar APC, Godwin Ikuru, ya yi hasashen samun nasara ga jam'iyya mai mulki
- Rahotanni sun yi nuni da cewa ana kallon takarar gwamnan jihar Kogi a matsayin tafi ƙarfi tsakanin ɗan takarar APC Ahmed Ododo da Sanata Dino Melaye
- Dino Melaye dai tsohon ɗan majalisar wakilai ne kuma ya taɓa yin sanata sau ɗaya a majalisar dattawa
Lokoja, jihar Kogi – Wanda ya kafa cocin Jehovah's Eye Salvation Ministry, fasto Godwin Ikuru, ya ce Ahmed Ododo, ɗan takarar jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a zaɓen jihar Kogi zaɓin Allah ne.
A ranar 11 ga watan Nuwamba, 2023 ne za a gudanar da zaɓen gwamnan jihar Kogi na 2023, domin zaben wanda zai ja ragamar jihar nan da shekara huɗu masu zuwa.
Gwamnan Arewa Ya Waiwayi Leburori, Ya Ce Zai Ɗauki Nauyin Karatunsu Har Su Gama Jami'a Bisa Sharaɗi 1
"Ododo shi ne zaɓin Allah": fasto Ikuru
Gwamna Yahaya Bello na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki ya zo ƙarshen wa'adin mulkinsa na biyu, kuma ba zai iya sake tsayawa takara a karo na uku ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai, yaronsa a siyasance Ododo, na cikin takarar kuma shi ne ɗan takarar jam'iyyar APC mai mulki a jihar.
Da yake yin hasashen gabanin zaɓen da ke tafe, fasto Ikuru a cikin wani faifan bidiyo da ya sanya a Facebook ya bayyana cewa:
"Ina mika wannan sako mai ƙarfi ga gwamnan jihar Kogi. Eh, zan kira shi gwamna domin shi ne Allah ya zaba. Eh, matashin da Yahaya Bello ya kawo, shi ne Allah ya zaɓa."
"Don haka, mutanen Kogi, sun san abin da za su yi."
Yahaya Bello Ya Bayyana Burinsa Bayan Ya Bar Mulki
A wani labarin kuma, gwamnan jihar Kogi na jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Yahaya Bello, ya bayyana babban burin da yake da shi da zarar ya yi bankwana da madafun ikon jihar.
Yahaya Bello ya bayyana cewa baya da wani buri wanda ya danganci siyasa, face kawai ya ga ya taimakawa gwamnatin shugaban ƙasa Bola Tinubu ta yi nasara wajen ciyar da al'ummar ƙasar nan gaba.
Asali: Legit.ng