Tinubu Ya Nada Adewale Adeniyi a Matsayin Shugaban Kwastam

Tinubu Ya Nada Adewale Adeniyi a Matsayin Shugaban Kwastam

  • Shugaba Bola Tinubu ya tabbatar da Adewale Adeniyi a matsayin kwantrola janar na Hukumar Kwastam ta Najeriya
  • An bayyana hakan ne cikin wata sanarwa mai dauke da sannun Wille Bassey, Direktan Watsa Labarai na ofishin SGF a ranar Juma'a 20 ga watan Oktoba a Abuja
  • Shugaban kasar ya bukaci Adeniyi ya yi amfani da gogewarsa da kwarewarsa a sabon mukamin da aka nada shi

Gidan Gwamnati - Shugaba Bola Tinubu ya nada Adewale Adeniyi (MFR( a matsayin Kwantrola Janar na Hukumar Hana Fasakwabri ta Kasa wato Kwastam.

Tinubu ya nada Adeniyi a matsayin Kwantrola Janar na Kwastam
Tinubu a ranar Juma'a 20 ga watan Oktoba ya nada Adeniyi a matsayin shugaban Kwastam. Hoto: Photo credit: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, @FMINONigeria
Asali: Twitter

Tinubu ya zaburar da Adeniyi

Nadin za ta fara aiki ne daga ranar 19 ga watan Oktoban 2023 kuma nadinsa ya yi dai-dai da dokokin ayyukan gwamnati, PSR.

Shugaban kasar ya bukaci shi ya yi amfani da kwarewa da gogewarsa a sabon mukamin da aka nada shi.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Tinubu Ya Amince Da Nadin Sabon Mai Binciken Kudi Na Kasa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan na kunshe cikin sanarwar da direktan watsa labarai na Sakataren Gwamnatin Tarayya, Willie Bassey, ya fitar a ranar Juma'a a shafin X na Ma'aikatar Labarai da Wayar da Kan Yan Kasa.

"Shugaban kasar ya umurce shi da ya kawo kwarewarsa mai yawa don yin amfani da shi a wannan sabon mukaminsa", wani sashi na sanarwar.

Tinubu Ya Nada Sabon Shugaban Bankin Masana'antu, BOI

Shugaba Kasan Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, a baya ya nada Dakta Olasupo Olusi a matsayin sabon Manaja kuma Babban Jami’in Bankin Masana’antuna Kasa (BOI).

Wannan sabon nadin na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa, Cif Ajuri Ngelale, ya fitar ranar Alhamis kuma aka wallafa a manhajar X wacce aka sani a Twitter a baya.

Sanarwan ta cigaba da cewa Shugaba Tinubu ya yi wannam nadin ne bayan tsohon shugaban bankin BOI, Mr Olukayode Pitan, ya yi murabus don ra'ayin kansa.

Kara karanta wannan

Reno Omokri Ya Yi Martani Yayin da Sheikh Gumi Ya Caccaki Wike Kan Hada Kai Da Isra’ila

Shugaba Tinubu Ya Nada Matashiya Yar Shekara 25 Mukami

A wani rahoton daban kun ji cewa Shugaba Bola Tinubu ya nada Fatima Faruk a matsayin babban mai bada shawara kan harkokin mata.

Sanarwar ya fito ne a shafin manhajar X na jam'iyyar All Progressives Congress, APC, reshen Birtaniya.

Jam'iyyar ta APC reshen Birtaniya ta fitar da sanarwar ne a ranar 16 ga watan Oktoban 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164