Sunayen Alkalai 7 da Za Su Yi Hukunci a Shari’ar Atiku, Obi v Tinubu a Kotun Koli
- An tsaida Alkalan da za su yi hukuncin karshe a kan shari’ar zaben shugaban kasar Najeriya na 2023 a kotun koli
- Macen farko da ta rike kotu a Yobe, Uwani Musa Abba Aji kadai ce mace a cikin Alkalan da kotun ta zabo su yi hukunci
- Muhammad Lawal Garba wanda ya tafi kotun koli bayan zaben 2019 ya samu wuri, haka zalika Adamu Adamu Jauro
Abuja - Kotun koli ta zakulo Alkalai bakwai da za su saurari shari’ar zaben shugaban kasa inda ake kalubalantar nasarar Bola Ahmed Tinubu.
Daily Trust ta tattaro jerin sunayen manyan Alkalan da za su yanke hukunci a karar da jam’iyyun ADP, LP da PDP su ka daukaka a kotun.
Alkalan da za su yi hukunci a kotun koli
1. John Inyang Okoro
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mai shari'a John Inyang Okoro zai jagoranci zaman a cewar The Nation. Alkalin ya fito ne daga Nung Ukim, Ikono da ke jihar Akwa Ibom.
Shi ne na hudu a jerin alkalan kotun koli, ya dare kujerarsa ne a Nuwamban 2013.
2. Uwani Musa Abba Aji
Uwani Musa Abba Aji mutumiyar jihar Yobe ce da aka haifa a 1956, ta yi karatu a jami’ar ABU Zariya a 1980, da ita za a yanke hukuncin zaben bana.
Ita kadai ce mace a jerin masu hukuncin, kuma macen da ta fi matsayi a kotun koli.
3. M. Lawal Garba
Muhammad Lawal Garba wanda ya ba Muhammadu Buhari nasara a karar zaben 2019 ya na kotun koli, da shi za a saurari shari’ar zaben 2023.
A shekarar 1981 ya zama lauya, ya rike Alkalin Alkalan Zamfara daga 1996 zuwa 2004.
4. Adamu Jauro
Alkalin ya na cikin wadanda su ka saba a shari’ar Ahmad Lawan da Bachir Machina da wasu karan PDP, asalinsa mutumin jihar Gombe ne.
Jauro mai shekara 64 ya yi aiki a manyan kotuna a Jos, Yola, Legas, Ibadan da Fatakwal.
5. I.N. Saulawa
Ibrahim Mohammed Musa Saulawa ya je kotun koli ne a 2020, kafin nan ya yi aiki tun daga kotun majistare zuwa kotun daukaka kara a Najeriya.
A lokacin da aka yi zaben shugaban kasa a 2007, Saulawa ya na kotun daukaka kara.
6. Tijjani Abubakar
Tijjani Abubakar ya na cikin Alkalan da NJC ta ba Muhammadu Buhari shawarar ya nada a matsayin Alkalan kotun koli a 2020, kuma haka aka yi.
Shi ma Alkalin kotun kolin ya fito ne daga Yobe, ya yi aiki a babban kotu da ke Legas.
7. Emmanuel Agim
Emmanuel Akomaye Agim ya taba zama Alkalin Alkalai a kasashen Gambiya da Swaizaland, babban Alkali ne da ake ji da shi a nahiyar Afrika.
Agim ya yi karatun LLB a Jami'ar Kalaba, daga nan ya tafi Legas har zuwa Birtaniya.
Atiku ya kai sababbin hujjoji
Ana da labari Atiku Abubakar yana nan a kan bakansa na gabatar da sababbin hujjoji kan Bola Tinubu wanda INEC ta ba nasara a zaben da aka yi.
Ɗan takarar shugaban ƙasar ya buƙaci kotun ƙoli ta amince ya gabatar da wasu hujjoji da za su nuna Tinubu ya yi karyar takardun karatunsa.
Asali: Legit.ng