Bayan Tsawon Lokaci, Tinubu Zai Jagoranci FEC, Za a Rantsar da Sababbin Ministoci
- Bisa dukkan alamu Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu za ta fara aiki gadan-gadan a makon nan a Najeriya
- FEC za ta zauna a fadar Aso Rock Villa, wannan zai zama na karon farko tun bayan an kaddamar Majalisar ministocin
- A taron wannan makon ake tunanin rantsar da sababbin ministoci daga Sanatoci su ka tantance a majalisar dattawa
Abuja - Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu zai yi zama da ministocinsa da sauran manyan jami’an gwamnatin tarayya a taron FEC.
Daga majiya mai karfi, tashar Arise TV ta samu labari cewa ana sa ran Mai girma Bola Ahmed Tinubu zai jagoranci majalisar FEC a yau.
Wannan zai zama karon farko da shugaban kasar ya yi wannan zama tun bayan rantsar da ministocinsa da ya yi a karshen watan Agusta.
Aikin da yake gaban majalisar FEC
Rahoton ya ce a zaman da za ayi na makon nan, shugaban Najeriyan zai duba wasu bukatu da ya amincewa sababbin ministocin kasar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ba a samu cikakken bayani game da zaman ba, amma ana sa ran fara taron ne da karfe 12:00 na rana dauke da duka ministoci kusan 50.
Wadanda su ke kusa da fadar shugaban kasar sun ce da wahala a fasa yin zaman a yau.
Ministocin Tinubu sun kama aiki
Bayan rantsar da ministoci a ranar 26 ga watan Agusta, da-dama daga cikinsu kama aiki, har wasu sun turo takarda zuwa ga fadar Aso Rock.
A wajen zaman za a tattauna a game da bukatun ministocin domin yanke hukunci.
Baya ga ministoci, Legit ta fahimci Sakataren gwamnati, shugaban ma’aikatar gwamnati, da shugaban ma’aikatan gwamnati za su halarci FEC.
Yadda Yan Sanda Suka Kama Fasto da Wasu Mutum 3 da Kokon Kan Dan Adam, Sun Fadi Abin da Za Su Yi da Shi
Nadin nadin sababbin Ministoci 3
Punch ta ce a zaman da za ayi yau ne za a rantsar da karin ministocin da aka tantance a majalisar dattawa, daga nan kuma sai su shiga ofis.
Karin ministocin su ne: Dr. Jamila Ibrahim Bio, Ayodele Olawande da Balarabe Abbas Lawal daga jihohin Kwara, Ondo da kuma Kaduna.
Hakan zai bada dama yawan ministocin Bola Tinubu ya karu daga 45 zuwa 48 a Najeriya.
Tinubu ya saba doka a nadin EFCC?
An ji labari Daniel Bwala wanda ‘Dan adawa ne, ya zargi shugaba Bola Tinubu da yin kaca-kaca da doka wajen yin nadin shugaban EFCC.
Bwala ya ce Olu Olukayode bai cancanci ya rike wannan mukami ba, sai dai fadar shugaban kasa ta maidawa shi da ire-irensa martani.
Asali: Legit.ng