Jam'iyyar APC Ta Dage Yakin Neman Zaben Gwamana a Jihar Bayelsa

Jam'iyyar APC Ta Dage Yakin Neman Zaben Gwamana a Jihar Bayelsa

  • Jam'iyyar APC ta ɗage gangamin kaddamar da yaƙin neman zaɓen ɗan takararta na gwamna a zaben Baylesa
  • Kakakin APC, Felix Morka, ya ce an ɗage kaddamar da kamfen daga ranar Asabar, za a sanar da sabuwar rana nan gaba
  • Wannan mataki na zuwa ne bayan babbar Kotun tarayya mai zama a Abuja ta hana tsohon ministan mai, Sylva, takara

FCT Abuja - Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta dage kaddamar da yakin neman zaben gwamnan jihar Bayelsa da aka shirya yi a ranar Asabar ɗin nan.

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta sanya ranar 11 ga watan Nuwamba domin gudanar da zaben gwamnoni a jihohin Bayelsa, Kogi da kuma Imo.

Shugaban APC na ƙasa, Ganduje da Timipre Sylva.
Jam'iyyar APC Ta Dage Yakin Neman Zaben Gwamana a Jihar Bayelsa Hoto: OfficialAPCNg
Asali: UGC

Jam’iyyar APC, wadda ta kaddamar da kamfen dinta a jihohin Kogi da Imo, ta zaɓi ranar Asabar, 14 ga watan Oktoba, 2023 domin buɗe fagen yakin neman zabenta a jihar Bayelsa.

Kara karanta wannan

'Dan Takarar Gwamnan PDP Ya Tsallake Rijiya da Baya Yayin da Aka Kai Masa Harin Kisa Sau 4 a Arewa

Amma mai magana da yawun APC ta ƙasa, Felix Morka, ya ce an ɗaga kaddamar da kamfen zaben gwamnan Bayelsa a wata sanarwa da ya sa wa hannu ranar Jumu'a.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwan wadda aka wallafa a shafin APC na manhajar X watau Twitter, ta ce za a sanar da sabuwar ranar buɗe fagen kamfe ɗin idan jam'iyyar ta cimma matsaya.

Sanarwan ta yi bayanin cewa:

"Jam'iyyar APC na sanar da dage kaddamar da yakin neman zaben gwamnan jihar Bayelsa da aka shirya gudanarwa a ranar Asabar 14 ga Oktoba, 2023 a Yenagoa, babban birnin jihar."
"Za a sanar da sabuwar ranar gangamin buɗe fagen kamfe a lokacin da ya dace da zaran an sanya sabon lokaci."

Meyasa jam'iyyar APC ta ɗage kamfen Bayelsa?

A halin da ake ciki, jam'iyyar APC ba ta bayyana ainihin dalilin da ya haddasa ta ɗage yaƙin neman zaɓe a Bayelsa ba.

Kara karanta wannan

Ganduje Ya Ƙara Turmushe Jam'iyyar Adawa Yayin da Ɗan Majalisa da Jiga-Jigai Suka Koma Bayan APC

Amma ana hasashen cewa ba zai rasa nasaba da soke takarar Timipre Sylva, ɗan takarar gwamna a inuwar APC, wanda babbar Kotun tarayya ta yi.

Shugaba Tinubu Ya Nada Sabon Shugaban FERMA da Majalisar Gudanarwa

Kun ji cewa Bola Ahmed Tinubu ya rushe majalisar gudanarwa ta hukumar kula da kyaun titunan gwamnatin tarayya FERMA.

Shugaban ya kuma amince da naɗa sabbin waɗanda zasu jagoranci hukumar na tsawon shekara huɗu masu zuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262