Dikko Radda, Mala Buni da Ragowar Gwamnoni da ba a Shari’ar Zabe da su a Kotu

Dikko Radda, Mala Buni da Ragowar Gwamnoni da ba a Shari’ar Zabe da su a Kotu

  • A farkon bana aka gudanar da zaben gwamnoni a jihohi 28 kamar yadda dokar kasa tayi tanadi
  • ‘Dan takara ya na da damar zuwa kotun karar zabe idan bai yarda da sakamakon hukumar INEC ba
  • Gwamna AbdulRahman AbdulRasaq ya na cikin wadanda ba a kalubalanci tazarcensu ba

Abuja - Rahoton nan ya kawo jerin jihohin da ‘yan takaran gwamnonin adawa ba su shigar da kara a zaben da aka gudanar a jihohin kasar nan ba.

Kamar yadda aka sani, idan mai shigar da kara ya yi nasara, kotun sauraron kararrakin zabe za ta tsige wanda aka rantsar a kan kujera.

Gwamnoni
Wasu Gwamnonin Najeriya a Kigali Hoto: www.maxilensnews.com
Asali: UGC

1. Gwamnan Jihar Kwara

Gwamna AbdulRahman AbdulRasaq bai samu kalubalen shari’a bayan nasarsa a zaben 2023 ba, abokan adawarsa ba su kai shi kotun zabe ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Dan Najeriya Da Ke Tuka Baro a Kasuwa Ya Zama Shahararren Farfesa Da Ake Ji Da Shi

Mai girma gwamnan ya yi fama da rikicin gida a APC kafin zabe, ya huta da kashe kudi a kotu domin Abdullahi Yaman ya rungumi kaddara.

2. Gwamnan Jihar Neja

Isa Liman Kantagi bai bata lokacinsa a zuwa kotun karar zabe ba bayan ya sha kashi a hannun Hon. Umar Sani Bago a zaben gwamnan Neja.

A lokacin da ake yakin zabe, ‘dan takaran PDP wanda ya zo na biyu ya yi barazanar cewa duk wanda ya ci kudinsa sai mutu idan bai zabe shi ba.

3. Gwamnan Jihar Yobe

Abdullahi Shariff ya nemi ya zama barazana ga Mai Mala Buni a zaben gwamnan Yobe, amma da ya sha kashi a zaben bai dauki matakin zuwa kotu ba.

Babu mamaki ratar kusan kuri’u 200, 000 da aka samu tsakanin PDP da APC ya sa alkalai ba su sha wahalar kafa kotun korafin zaben gwamna a Yobe ba.

Kara karanta wannan

Jerin Gwamnonin Da Kotun Zabe Ta Tsige Cikin Wata 5 Da Dalili

4. Gwamnan Jihar Katsina

Dr. Dikko Umaru Radda ya ba Sanata Yakubu Lado Danmarke ratar kuri’u fiye da 370, 000 a zaben gwamnan jihar Katsina da aka yi a watan Maris.

Yakubu Lado Danmarke wanda ya shiga takarar gwamna a jihar Katsina sau uku bai shigar da kara a kotu ba, hakan ya saukakawa Gwamna Radda.

Shari'ar zabe a Kano

Hon. Nasiru Sule Garo wanda tsohon ‘dan majalisar wakilan tarayya ne ya rasa kararsa a kotun zabe kamar yadda rahoto ya zo kwanakin baya.

Kotun sauraron karar zabe ta ce jam’iyyar APC da ‘dan takaranta su ka yi galaba a zabe, ‘Dan Kwankwasiyyan ya na cikin kwamishoni masu ci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel