Babu Rudani a Kaduna Kan Hukuncin Kotun Zabe – Gwamna Uba Sani
- Gwamnan Kaduna, Uba Sani ya bayyana cewa babu wani rudani a hukuncin da kotun zaben gwamnan jihar ta yanke
- A ranar Alhamis, 28 ga watan Satumba ne kotun zaben gwamnan jihar Kaduna ta yi watsi da karar PDP da dan takararta, Isah Ashiru kan nasarar Sani
- Uba Sani ya zargi PDP da batar da manyan gidajen jaridu ta hanyar basu bayanan da suke ba daidai ba
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Kaduna - Gwamnan jihar Kaduna kuma dan takarar jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a zaben ranar 18 ga watan Maris, Uba Sani ya ce babu wani rudani a hukuncin kotun zabe na ranar Alhamis, wacce ta kori karar jam'iyyar PDP da Isah Ashiru kan nasararsa.
Sani ya bayyana hakan ne yayin hira da Channels TV a shirin Politics Today a ranar Alhamis, 28 ga watan Satumba.
Ku tuna cewa kotun zaben ta ce da ace ba a kori karar saboda rashin inganci ba, da ta yi umurnin sake zabe a rumfunan zabe 22 cikin kwanaki 90.
Wasu rahotannin kafafen yada labarai sun yi ikirarin cewa kotun ta tsige dan takarar na jam’iyyar All Progressives Congress (APC).
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Babu wani rudani a hukuncin kotun zabe, Uba Sani
Sani ya ce:
"Ina ganin babu rudani a wurin. Kamar yadda na bayyana, ga wasu daga cikinmu da ke da hannu a daftarin dokar zabe, babu wani abu mai kama da rudani a wurin.
"An yi watsi da karar saboda rashin cancanta. Abu na farko da karar an yi shi a wajen lokaci. Kuma shakka babu, idan ka duba dokar zabe, wannan kadai ya jefa shari'arsu a kwandon shara. Wannan na bisa doka. Akwai shari'o'i da dama irin wannan."
Gwamnan ya bayyana cewa jam'iyyar na iya yin nasara a gwagwarmayar zabe "ko ka yi nasara a gwagwarmayar farfaganda."
Sani ya yi zargin cewa PDP "ta batar da wasu manyan gidajen jaridu kuma sun matukar bani kunya."
Ya nuna rashin jin dadi kan abun da ya bayyana a matsayin azarbabin "manyan gidajen jaridu" na sakin labarai ba tare da jiran hukuncin karshe ba, rahoton Vanguard.
Sani, yayin da ya yi kira da a yi taka-tsan-tsan, ya bayyana cewa bai kamata a yi kasa a gwiwa ba wajen neman ‘yancin fadin albarkacin baki ta kafafen sada zumunta, domin a cewarsa ya kamata a bar mutane su bayyana ra’ayoyinsu.
PDP ta yi nasara, kotu ta yanke hukunci kan zaben gwamna a 2023
A wani labarin, mun ji cewa kotun sauraron korafe-korafen zaben gwamnan jihar Delta, ta tabbatar da Gwamna Sheriff Oborevwor a matsayin halastaccen gwamnan jihar.
Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da dan takararta, Sanata Ovie Omo-Agege, ne suka shigar da kara gaban kotun suna kalubalantar nasarar Oborevwor na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben 2023 da ya gabata.
Asali: Legit.ng