"Ba Zaka Iya Kai Tinubu Ga Nasara Ba a 2027" Kwankwaso Ya Caccaki Ganduje
- Sanata Rabiu Kwankwaso ya maida zazzafan martani ga Ganduje kan kalaman da ya yi cewa shi babban mara nasara ne
- Jagoran NNPP na ƙasa ya yi ikirarin cewa Ganduje ba zai kai shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ga tudun nasara ba a zaɓen 2027
- Ya kuma yi gargaɗin cewa duk wata manaƙisa ta kwace Kano ba zata kai ga nasara ba Kanawa da Alkalai zasu wargaza ta
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Kano - Jagoran NNPP na ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a zaben da ya wuce, Rabiu Kwankwaso, ya caccaki babban abokin faɗansa, Abdullahi Ganduje.
Kwankwaso ya ce Ganduje ya zama kaya ga APC kuma ba zai iya jagorantar nasarar shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ba a baban zaɓen 2027.
A wata sanarwa da kakakin NNPP na ƙasa, Yakubu Shendam, ya fiyar ya maida martani ga wasu kalamai da suka fito daga bakin Ganduje, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
A kalaman, Ganduje, shugaban APC na ƙasa ya kira Kwankwaso da riƙaƙƙen mara nasara wanda ba zai iya cin zaɓen shugaban ƙasa ba, Vanguard ta ruwaito.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
NNPP ta maida martani
Sanarwan ta ƙara da cewa almundahanar da ake zargin tsohon gwamnan Kano, Ganduje da aikatawa, "Ba zata gyaru ba kuma ba zai iya kai Tinubu da APC ga nasara ba a 2027.
"Matukar Ganduje na matsayin shugaban jam'iyya na ƙasa, to tuntuni APC ta zama gawa. Ku yarda ko kar ku yarda, Ganduje kaya ne ga Tinubu, APC da ƙasa baki ɗaya."
"Kuma matuƙar Ganduje na nan a matsayin shugaban APC ta ƙasa, Bola Tinubu ba zai kai labari ba a zaɓen shugaban ƙasar 2027, buga shi za ai da ƙasa."
Sanarwar ta kuma nuna cewa Ganduje bai taba cin zabe ba a tsawon rayuwarsa sai wanda Kwankwaso ya tsaya masa a matsayin gwamna a zaɓen 2015.
Kungiyar TUC Ta Yi Kakkausar Martani Ga Tinubu Kan Alkawuran Karya Da Ya Ke Yi, Ta Fadi Matakin Gaba
Sau 14 ina cin nasara a zaɓe - Kwankwaso
Kwankwaso, tsohon gwamnan jihar Kano, ya bayyana cewa ya tsaya takara sau 17 kuma ya samu nasara sau 14 daga cikin wadannan lokutan.
Jagoran NNPP ya kuma koka kan abin da ya kira yunkurin APC mai mulki karkashin jagorancin Ganduje na yin ƙarfa-ƙarfa da kwace muradun al’ummar jihar Kano.
Ya kuma yi gargaɗin cewa duk wani yunƙuri da zasu yi na kwace Kano kamar yadda suka yi a 2019 zai fuskanci tirjiya daga Kanawa da kuma Alƙalai na gari.
Tashin Hankali Yayin da Gwamnan Delta Zai San Makomarsa Gobe Jumu'a
A wani rahoton kuma An shiga yanayin tashin hankali yayin da Kotun zaɓe ta ce zata yanke hukunci kan zaben gwamnan jihar Delta gobe Jumu'a.
Manyan jam'iyyun adawa APC, LP da SDP ne suka shigar da ƙara suna masu ƙalubalantar nasarar gwamna Oborevwori na PDP.
Asali: Legit.ng