Jandor Da PDP Sun Yi Watsi Da Hukuncin Kotun Zaben Gwamnan Lagas, Za Su Dauki Mataki
- Jam'iyyar PDP reshen jihar Lagas da dan takararta na gwamna, Olajide Adediran wanda aka fi sani da Jandor, sun yi watsi da sakamakon hukuncin kotun zabe
- Jam’iyyar da Jandor sun caccaki hukuncin kotun da ya tabbatar da zaben Babajide Sanwo-Olu da mataimakinsa, Obafemi Hamzat
- Dan takarar jam'iyyar adawan ya yi Allah wadai da hukuncin kotun zaben, yana mai cewa ba shi da sahihanci
Ikeja, Jihar Lagos - Dan takarar gwamnan jam'iyyar Peoples Democratic Party a jihar Lagas a zaben 2023, Olajide Adediran, wanda aka fi sani da Jandor, ya yi watsi da sakamakon hukuncin kotun zaben.
A ranar Litinin, 25 ga watan Satumba, Jandor ya nuna rashin gamsuwarsa kan hukuncin kotun zaben jihar wacce ta tabbatar da nasarar dan takarar jam'iyyar All Progressives Congress, Babajide Sanwo-Olu.
Da yake martani a kan lamarin, Jandor, a cikin wata sanarwa daga kakakinsa, Gbenga Ogunleye, ya ce hukuncin abun takaici ne, rahoton Punch.
Dan takarar gwamnan ya bayyana cewa kotun zaben ta ki duba sahihanci da kwararan hujjojin da tawagar lauyoyinsa (Jandor) suka gabatar mata don kalubalantar cancantar yan takarar APC da Labour Party.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ya kara da cewar hukuncin kotun zaben ya ci karo da tanadin kundin tsarin mulki da dokar zaben 2022, musamman kan batutuwan da suka shafi cancantar dan takara a zabe.
Wani bangare na jawabin na cewa:
"Wannan ba shine karshen tsarin zaben ba, kawai dai wani mataki ne. Za mu yi nazarin hukuncin sannan mu dauki matakai wanda zai dace da ra'ayin yan Lagas."
Kotun zaben gwamnan Lagas ta yanke hukunci a kan nasarar Sanwo-Olu
A baya mun ji cewa kotun da ke sauraron karar zaben gwamnan jihar Lagas ta zartar da hukunci kan kararrakin da ke kalubalantar nasarar gwamnan jihar, Babajide Sanwo-Olu.
A yayin zaman yanke hukuncin da aka yi a ranar Litinin, 25 ga watan Satumba, kotun ta yi fatali da karar da Gbadebo Rhodes-Vivour da Labour Party suka shigar don kalubalantar nasarar APC da dan takararta a zaben.
Hakazalika, kotun zaben ta kuma kori karar da Olajide Adediran wanda aka fi sani da Jandor da jam'iyyarsa ta PDP, suka shigar duk don kalubalanar Sanwo-Olu a zaben.
Asali: Legit.ng