Kotu Ta Bayyana Wanda Ya Yi Nasara a Zaben Mazabar Amuwo-Odofin II Ta Jihar Legas

Kotu Ta Bayyana Wanda Ya Yi Nasara a Zaben Mazabar Amuwo-Odofin II Ta Jihar Legas

  • An samu wanda ya yi nasara a zaben majalisar dokokin jihar Legas, Amuwo-Odofin II da aka gudanar a ranar 18 ga Maris, 2023.
  • Kotun da ke zamanta a Legas ta bayyana Rauf Olawale Sulaiman, dan takarar jam’iyyar APC a matsayin zababben dan majalisa mai inganci a mazabar.
  • Kotun ta soke sakamakon INEC a hukuncin da ta yanke, inda ta ce dan takarar jam’iyyar LP, Olukayode Doherty, bai cancanci tsayawa takara ba.

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Legas - Kotun sauraren kararrakin zabe ta Majalisar Dokokin Jihar Legas ta bayyana Rauf Olawale Sulaiman na Jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben Majalisar Dokokin Jihar Legas, Amuwo-Odofin II da aka gudanar a ranar 18 ga Maris, 2023.

Jaridar Guardian ta kawo rahoto cewa kotun da ke zamanta a dandalin Tafawa Balewa (TBS) a lokacin da take yanke hukunci, ta umarci hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta gabatar da Sulaiman takardar shaidar cin zabe a matsayin wanda ya lashe zaben.

Kara karanta wannan

Bayan Abba Gida-Gida, Kotun Zabe Ta Ƙara Yanke Hukunci Kan Nasarar Gwamnan PDP a Arewa

Kotu ta kwace kujerar dan majalisar LP a Legas
Kotu soke zaben dan majalisar Labour Party a jihar Legas Hoto: Leadership
Asali: Facebook

Meyasa kotun ta ƙwace nasarar ɗan takarar LP?

A yayin gabatar da hukunci, kwamitin mutum uku karkashin jagorancin Mai shari’a Ashu Ewah, ya bayyana cewa dokar zabe ta 2022 ba ta yarda a bayyana dan takara a matsayin wanda ya lashe zaben ba idan dan takarar bai cika shiga harkar zaben ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kotun ta yanke hukuncin cewa dan takarar jam’iyyar Labour (LP), Olukayode Doherty, wanda hukumar zabe ta INEC ta ba shi satifiket bai bayyana a zaben ba, don haka bai cancanci tsayawa takara ba.

Kotu ta sa ranar yanke hukunci kan shari'ar gwamnan Legas

Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan jihar Legas ta sanya ranar da za ta yanke hukunci kan shari'ar zaɓen gwamnan jihar Legas.

Kotun ta bayyana cewa za ta zartar da hukuncinta a ranar Litinin, 25 ga watan Satumban 2023.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Kotu Ta Yanke Hukunci, Ta Fadi Wanda Ya Lashe Zaben Gwamna a Jihar Bauchi

Kotu Ta Tabbatar Da Nasarar Gwamna Alia

A wani labarin kuma, kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan jihar Benue ta tabbatar da nasarar da gwamna Hyacinth Alia na jam'iyyar APC ya samu a zaɓen gwamnan jihar na ranar 18 ga watan Maris.

Kotun ta yi fatali da ƙarar da jam'iyyar PDP da ɗan takararta Titus Uba suka shigar suna ƙaƙubalantar nasarar gwamnan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng