Yakubu Shendam: NNPP Ta Nada Sabon Mai Magana da Yawunta Na Kasa

Yakubu Shendam: NNPP Ta Nada Sabon Mai Magana da Yawunta Na Kasa

  • Jam'iyyar NNPP ta naɗa sabon mai magana da yawunta na ƙasa jim kaɗan bayn martani kan hukuncin tsige Abba Gida-Gida
  • NWC karkashin jagorancin Abba Kawu ya amince da naɗin Yakubu Shendam a matsayin sabon Sakataren yaɗa labarai na NNPP
  • Shendam ya nuna jin daɗinsa da wannan matsayi kuma ya nemi haɗin kan kowa domin ciyar da jam'iyyar gaba

FCT Abuja - Jam’iyyar NNPP karkashin jagorancin kwamitin ayyuka na kasa (NWC), ta nada Yakubu Shendam, a matsayin sabon Sakataren yada labaranta na kasa.

Jaridar Punch ta ce NNPP ta bayyana haka ne jim kaɗan bayan kammala jawabi ga 'yan jarida game da hukuncin da Kotu ta yanke kan zaben gwamnan Kano a Abuja.

Jam'iyyar NNPP ta nada sabon kakakinta na ƙasa.
Yakubu Shendam: NNPP Ta Nada Sabon Mai Magana da Yawunta Na Kasa Hoto: NNPP
Asali: UGC

Wannan dai na zuwa ne yayin da NNPP karkashin jagorancin Abba Kawu ta kori tsohon kakakin jam’iyyar, Agbor Major, tare da wasu fitattun shugabanninta na ƙasa.

Kara karanta wannan

APC Ta Yi Martani Bayan Atiku Ya Samu Nasara Kan Shugaba Tinubu a Kotu, Ta Bayyyana Abin Da Hakan Ke Nufi

Sakataren NNPP na kasa, Mista Olaniyoku Dipo, shi ne ya bayyana wanda aka naɗa a madadin mukaddashin mataimakin shugaban jam’iyyar na kasa, Nwaeze Onu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce naɗin sabon kakakin jam'iyya wanda kwamitin zartarwa na ƙasa (NEC) ya amince da shi, zai fara aiki ne nan take, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Mista Dapo ya ce:

"Jam’iyyar NNPP tana sanar da ku cewa ta yi sabon kamu a cikin 'ya'yanta, sabon shugaban da zai yi aiki a matsayin Sakataren Yada Labarai na Kasa."
"Kuna iya tuntuɓarsa a ko da yaushe, kuna iya tambayarsa komai game da jam'iyyar NNPP, a shirye yake ya amsa muku a ko wane lokaci."

Sabon kakakin NNPP ya nuna farin cikinsa

Da yake maida martani kan naɗin da aka masa, Mista Shendam ya nuna jin dadinsa da kasancewa daya daga cikin mambobin NWC na jam’iyyar.

Kara karanta wannan

Kotun Zabe Ta Tsige Abba Gida-Gida Daga Kujerar Gwamnan Kano, Ta Faɗi Wanda Ya Ci Zaɓe

“Na ji dadin kasancewa a nan kuma ina so in tabbatar muku da cewa za mu yi aiki tare domin daukaka jam’iyyar NNPP tare da goyon bayanku, dole ne mu hada kai don ci gaban wannan jam’iyyar."

Kotun Zabe Ta Kwace Kujerun 'Yan Majalisar PDP Uku a Jihar Filato

A wani rahoton kuma Kotun zabe mai zama a Jos ta sauke yan majalisar dokokin jihar Filato guda uku na jam'iyyar PDP ranar Alhamis.

Kwamitin alkalan Kotun ƙarƙashin mai shari'a Muhammad Tukur, ya ce Kotu ta tsige su ne saboda PDP ba ta da ikon tsayar da 'yan takara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel