Kwana 100: Kotun Zabe Ta Tsige 'Yan Majalisar Wakilai 25, Sanatoci 5 Na APC, PDP, LP da NNPP

Kwana 100: Kotun Zabe Ta Tsige 'Yan Majalisar Wakilai 25, Sanatoci 5 Na APC, PDP, LP da NNPP

  • Sama da kwanaki 100 bayan rantsar da majalisar tarayya ta 10, aƙalla 'yan majalisar wakilai 25 da sanatoci 5 Kotu ta tsige daga kujerunsu
  • Jam'iyyar APC ce ta fi kowace jam'iyya rasa sanatoci yayin da kuma ita ce ta fi amfana da hukuncin kwace kujerun mambobin majalisar wakilai
  • Wani lauya Najeriya ya shaida wa Legit Hausa cewa duk da Kotun Zaben ta yanke hukunci, akwai damar ɗaukaka ƙara

FCT, Abuja - Akalla mambobin majalisar wakilan tarayya 25 da sanatoci 5 suka rasa kujerunsu kawo yanzu a kotun sauraron ƙorafe-korafen zaɓe a faɗin Najeriya.

Yayin da jam'iyyar APC ce kan gaba wajen rasa kujerun Sanatoci a hukuncin da kotu ta yanke, a ɗaya bangaren kuma ita ta fi amfana da hukuncin kwace kujerun mambobin majalisar wakilai.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP a Arewa Ya Maida Martani Bayan Kotun Zabe Ta Yanke Hukunci Kan Nasarar Da Ya Samu a 2023

Yadda hukuncin Kotun zabe ya kasance bayan kwanaki 100.
Kotun Zabe Ta Tsige 'Yan Majalisar Wakilai 25, Sanatoci 5 Na APC, PDP, LP da NNPP Hoto: APC Nigeria, PDP Update
Asali: Twitter

Waannan ta faru ne duk a cikin kwanaki 100 bayan magatakardan majalisar dattawa da na Majalisar Wakilan Tarayya sun rantsar da majalisa ta 10.

A halin yanzu, mafi akasarin 'yan Majalisun da suka yi rashin nasara a Kotu na jam'iyyun APC, PDP, Labour Party da NNPP mai kayan marmari sun lashi takobin ɗaukaka ƙara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanatocin da APC da PDP suka rasa zuwa yau

A mazaɓar Sanatan Kogi ta gabas da na Kogi ta tsakiya, Kotun zaɓe ta soke nasarar jam'iyyar APC mai mulki, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Haka nan kuma jam'iyyar APC ta sake rashin nasara a Kotu, inda aka rushe nasarar Sanatocinta a mazaɓar Delta ta tsakiya da kuma Delta ta kudu.

Bayan haka Kotun zaɓe ta rushe nasarar jam'iyyar PDP a mazaɓar Sanatan jihar Filato ta kudu.

Kara karanta wannan

Bayan Abba Gida-Gida, Kotun Zabe Ta Ƙara Yanke Hukunci Kan Nasarar Gwamnan PDP a Arewa

Jerin jihohin da za a gudanar cikon zaɓe

Kotun zaɓe ta umarci hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta shirya ƙarishen zabe a mazaɓar Delta ta tsakiya, Delta ta kudu da Kogi ta gabas cikin kwanaki 90 masu zuwa.

A ɗaya bangaren, Kotun ta tsige mambobin majalisar wakilan tarayya 26 zuwa yanzu, sai dai Kotun ɗaukaka ƙara mai zama a Abuja ta maida ɗaya daga cikinsu.

Jam'iyyar PDP ta rasa mambobin majalisar wakilai 12 yayin da Labour Party ta rasa guda 10. Jam'iyyar APC da kuma NNPP sun rasa ɗai-ɗai.

Wani lauya a Najeriya, Barista Tukur Badamasi, ya shaida wa Legit Hausa cewa duk da alƙalai sun yanke hukunci, doka ta bai wa mai ƙara ko wanda ake ƙara damar ɗaukaka ƙara.

"A siyasar Najeriya wannan ba sabon abu bane, idan baka gamsu da hukuncin da Kotu ta yanke ba, kana da damar ɗaukaka ƙara, wanda na san mafi yawanci za su tafi gaba."

Kara karanta wannan

Babbar Magana: Hukumar DSS Ta Kama Ɗan Majalisar PDP Bisa Zargin Hannu a Kashe Rayuka Sama da 20

"Yau nake ganin labarin Atiku Abubakar ya tafi Kotun ƙoli, to kamar haka yan majalisu suna da wannan damar. Alkali na duba hujjojin da aka gabatar masa ne wajen yanke hukunci."

A cewarsa, bai kamata mutane su riƙa zargin Kotu da fifita wani ɓangare ba saboda tana duba hujjoji da kuma tanadin dokoki ta yanke hukunci a kowace shari'a.

Kotu Ta Tsige Dan Majalisar PDP, Ta Tabbatar da Nasarar 'Yan Takarar APC 2 a Taraba

A wani rahoton kuma Kotun zabe mai zama a Jalingo ta kwace kujerar dan majalisar dokokin jihar Taraba na jam'iyyar PDP.

Bugu da ƙari, Kotun ta tabbatar da nasarar wasu 'yan takarar jam'iyyar APC a zaben mambobin majalisar jihar da ya gabata ranar 18 ga watan Maris, 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262