Shugaba Tinubu Ya Nada Sabbin Hadimai 18 a Ofishin Kashim Shettima
Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya amince da naɗin sabbin hadimai 18 a ofishin mataimakin shugaban ƙasa, Sanata Kashim Shettima.
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Tinubu ya amince da nadin masu ba da shawara na musamman da manyan mataimaka 18 domin aiwatar da kudirin gwamnatinsa a sassa daban-daban na tattalin arziki.
Wannan na ƙunshe ne a wata sanarwa da Shettima ya wallafa a shafinsa na manhajar X ranar Litinin mai ɗauke da sa hannun daraktan yaɗa labarai na ofishinsa.
Sabbin hadiman sun ƙunshi masu ba da shawara na musamman 6 da manyan masu taimakawa na musamman guda 12, jumulla su 18 kenan.
Sanarwan ta ƙara da bayanin cewa dukka zasu yi aiki ne a ofishin mataimakin shugaban ƙasa domin tabbatar da kudirin "Sabunta fata" na gwamnatin Bola Tinubu.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Jerin sunaye da muƙaman sabbin hadiman
Legit Hausa ta tattaro muku sunaye da muƙaman sabbin hadiman guda 18, ga su kamar haka:
1. Rukaiya El-Rufai - Mai bada shawara ta musamman kan NEC da sauyin yanayi
2. Tope Kolade Fasua - Mai bada shawara na musamman kan harkokin tattalin arziƙi.
3. Aliyu Modibbo Umar - Mai bada shawara na musamman kan ayyuka
4. Hakeem Baba Ahmed - Mai bada shawara na musamman kan harkokin siyasa
5. Jumoke Oduwole - Mai bada shawara na musamman kan PEBEC da hannun jari
6. Sadiq Wanka - Mai bada shawara na musamman kan samar da wutar lantarki
7. Usman Mohammed - Babban Mataimaki na musamman kan harkokin Gudanarwa
8. Kingsley Stanley Nkwocha - Babban mataimaki na musamman kan harkokin yada labarai da sadarwa.
9. Ishaq Ahmed Ningi - Babban mataimaki na musamman kan kafofin watsa labarai da ayyukan gaggawa
10. Peju Adebajo - Babban mataimaki na musamman kan Zuba Jari da cefanar da kayayyaki
11. Mohammed Bulama - Babban mataimaki na musamman kan Ayyuka na Musamman
12. Kingsley Uzoma - Babban mataimaki na musamman kan Kasuwancin Noma da samarwa
13. Gimba Kakanda - Babban mataimaki na musamman kan nazari da Bincike
14. Temitola Adekunle-Johnson - Babban mataimaki na musamman kan Samar da Ayyuka da MSMEs
15. Nasir Yammama - Babban mataimaki na musamman kan harkokin kirkire-kirkire
16. Zainab Yunusa - Babbar mataimakiya ta musamman kan majalisar tattalin arziki NEC
17. Mariam Temitope - Babbar mataimakiya ta musamman kan shirye-shiryen raya yanki
18. Bashir Maidugu - mataimakin mai ba shugaban kasa shawara (Babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa).
Sanatan Jam'iyyar PDP a Jihar Edo Ya Sake Koma Wa Jam'iyyar APC
A wani rahoton na daban Tsohon ɗan majalisar dattawan Najeriya, Sanata Mathew Urhoghide, ya sake koma wa jam'iyyar APC.
Sanata Urhoghide ya tattara kayansa ya fice daga jam'iyyar PDP zuwa APC ne ranar Litinin, 18 ga watan Satumba, 2023.
Asali: Legit.ng