Mai Neman Gwamna Ya Zama Hadimi Da Aka Cusa ‘Dan Takaran NNPP a Gwamnati

Mai Neman Gwamna Ya Zama Hadimi Da Aka Cusa ‘Dan Takaran NNPP a Gwamnati

  • Sheriff Oborevwori ya rantsar da wasu masu ba shi shawara, har ‘yan adawa sun samu mukami a Delta
  • Gwamnan jihar Delta ya nada Goodnews Agbi a cikin masu ba shi shawara duk da adawar da yayi masa
  • Sabon mai bada shawarar ya nemi kujerar Gwamna a NNPP a zaben 2023, amma bai iya doke PDP ba

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Delta - Gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborevwori ya rantsar da Goodnews Agbi a cikin masu ba shi shawara na musamman a mulki.

Daily Trust ta kawo wannan rahoto a yammacin Laraba, abin sha’awar shi ne Goodnews Agbi ya na cikin abokan adawar gwamnan.

Da aka tsaya takarar gwamnan Delta a zaben bana, Agbi ya nemi takara a karkashin jam’iyyar NNPP mai alamar kayan marmari.

Masu ba Sheriff Oborevwori shawara
'Dan NNPP ya zama Mai ba Gwamnan Delta shawara Hoto: @RtHonSheriff
Asali: Twitter

A karshe Sheriff Oborevwori ya yi galaba a karkashin jam’iyyar PDP mai rike da jihar tun 1999.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Gwamnan APC Ya Rantsar da Sabbin Kwamishinoni 37 da Hadimai a Jiharsa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sauran hadiman Gwamnan Delta

Sauran wadanda su ka shiga cikin sahun masu ba gwamnan shawara su ne: Hon. Charles Oniyere; Michael Ogboru; da Ebikeme Clark.

Sannan masu bada shawarar su ne: Cif Sylvester Oromoni, Hon. Shadrach Rapu, Dr. Donald Peterson, Peter Uviejitobor da Nathaniel Igbani.

Za a ga amfanin zaben PDP a 2023?

Mai girma gwmanan ya sha alwashin kawo sauyin da ba a taba gani ta fuskar abubuwan more rayuwa da cigaban tattalin arziki.

Gwamnan ya yi alkawari mulkinsa zai tafi da kowa, sannan zai kawo cigaba mai dorewa.

Dalilin jawo Agbi da takwarorinsa

Mai girma Oborevwori yake cewa wadanda ya ba mukamin masu bada shawara kwararru ne da su ka yi fice a wajen ayyukansu.

Gwamnatin Oborevwori ta na fatan Goodnews Agbi da sauran abokan aikinsa za su aiwatar da manufofin sabuwar gwamnatin Delta.

Kara karanta wannan

Ana Binciko Mutanen da ke da Alaka da Emefiele a Badakalar Naira Tiriliyan 7 a CBN

Agbi ba shi ne ‘dan takaran gwamnan farko da ya ja da baya ya karbi mukami a jam’iyya mai-ci ba, an ga irin haka a jam’iyyar APC.

Salihu Tanko Yakasai wanda ya bar APC zuwa jam’iyyar hamayya ta PRP ya jefar da mabudinsa, da alama ya sake sauya shekar siyasa.

Yakasai ya kuma karbar aiki a matsayin mai taimakawa shugaban APC wajen harkar yada labarai watanni bayan an fatattake shi.

Rikicin Kwankwasiyya da NNPP

Dazu mu ka samu rahoto cewa wani Lauya ya ankarar da INEC cewa Rabiu Kwankwaso da mutanensa su na yi wa NNPP shisshigi.

An bukaci hukumar INEC ta yi watsi da shirin ‘Yan Kwankwasiyya na canza dokoki da tambarin NNPP, da sunan ba su da ikon yin hakan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng