Sallamar Salihu Tanko Yakasai daga matsayin hadimin Ganduje ya janyo cece-kuce

Sallamar Salihu Tanko Yakasai daga matsayin hadimin Ganduje ya janyo cece-kuce

- Sallamar Salihu Tanko Yakasai, hadimin gwamna Abdullahi Ganduje da gwamnatin jihar Kano tayi ta haddasa cece-kuce a shafin soshiyal midiya

- Mutane da dama na ganin ba a kyauta wa Yakasai ba don kawai ya bayyana ra'ayinsa a matsayinsa na dan kasa mai yanci

- Ganduje dai ya sallami Dawisu ne saboda cigaba da caccakar gwamnatin APC wanda ita yake yi ma aiki

A yau Asabar, 27 ga watan Fabrairu ne gwamnatin Kano ta hannun kwamishinan watsa labarai na jihar, Mallam Muhammad Garba ta fitar da sanarwar dakatar da Salihu Tanko Yakasai daga matsayin hadimin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje.

Gwamnan ya ce ya sallami Yakasai ne saboda cigaba da yin maganganu wadanda ba su dace ba da suka sha ban-ban da alkibilar jam'iyyar APC da gwamnatinta da ya ke yi wa aiki.

Ya ce hadimin gwamnan ya gaza banbance tsakanin ra'ayinsa ka kashin kansa da kuma matsayar gwamnati a kan batutuwan da suka shafi jama'a da kasa baki daya.

Sallamar Salihu Tanko Yakasai daga matsayin hadimin Ganduje ya janyo cece-kuce
Sallamar Salihu Tanko Yakasai daga matsayin hadimin Ganduje ya janyo cece-kuce Hoto: Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR/Facebook, @dawisu/Twitter
Asali: UGC

KU KARANTA KUMA: Satar ‘yan matan Zamfara: Buhari gargadi gwamnoni kan saka wa 'yan fashi da kyautar kudi

Wannan baya rasa nasaba da caccakar gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari da na APC da Yakasai yayi bayan samun labarin sace yan matan GGSS Jangebe da aka yi a Zamfara.

Tuni dai jama’a suka fara bayyana ra’ayinsu a kan tsige Yakasai da Ganduje yayi, inda Legit.ng ta tattaro wasu da cikin sharhin da mabiya shafinta na Facebook suka yi.

Ga su nan a kasa:

Salisu Usman ya ce:

“Kuma sai mi dan an sallame shi tunda ba Allah ne yace baya son sa ba ai da dama.”

Kabiru Sani ya ce:

“Dama nasan arina wai an saci zanin mahaukaciya, nan da wata biyu kuma ya sake dawo da shi. Ganduje gandu aika-aika. Kuma ta tabbata babu wani freedom of speech kenan.”

Sanation NG Nationalist ya ce:

“Allura ta tono Garma, Kaza garin tone-tone ta tono hukar yankan ta, Yawan magana yasa aka sauke dan kama daga mai unguwar yankinsa, Kai yanzu jahar kano bama son yawan surutu. Hhhh”

Alh Karami ya ce:

“Wato yanzu andaina fadar gaskiya kenan idan kana cikin government ko. To in Allah ya yarda shima sai yazama gwamna.”

Dahiru S Dantsoho ya ce:

“Shikenan indankabaso atafi dakai a gwamnati to kagoyi bayan kisanda akewa talakawa, bakomi insha Allahu abunzaizo kanku indai kujeran mulkine abukaman kujeran wanzamine wannan yasauka wannan yahau, Allah shikyauta.”

Muhammad Sagir ya ce:

“Idan Hagu ta Kiya a koma dama,kwankwaso ya dauke shi matsayin sabon hadimin shi.”

Musa Adam ya ce:

“Wan nan matashi Allah yai maka albarka yasa kagama da iyayan ka lfy kuma ina ma addu"a, Allah yasa kafi haka Allah yasa kayi gwamnan kano.”

Mohd Auwal ya ce:

“Hhhh Ai munufar APC din kenan duk gwagwarmayar da yayi gashi an saka masa da mummunan karshe an koreshi daga aiki an daure shi . Ko ya maganar nanta right speech.”

Tukur Bakabe ya ce:

“Wanna Abin Yanuna Cewa Dukk Abinda 'Yan Siyasa Keyi Badon Talakawan Kasa Sukeyiba Dagga Fadin Gaskiya Sai Abiyo Mutun Har Gida Akamashi Wannan Ba dimokaradiya Bace.”

Mai Jonde Jam Sniper ya ce:

“Ka fadi gasky, kome ta janyo ma alkhairi ne insha Allaah.”

A gefe guda, mun kawo cewa Alhaji Tanko Yakasai, jigo a kungiyar dattawan Arewa kuma uba ga mai taimaka wa Ganduje kan harkokin yada labarai, Salihu Tanko Yakasai ya tabbatar da cewa dansa (Salihu) yana tsare a hannun jami’an tsaro.

KU KARANTA KUMA: Yanzu-yanzu: 'Yan bindiga sun sake komawa Kagara, sun bindige mutum hudu har lahira

Kodayake, bai bayyana takamaiman hukumar tsaron da ta tsare dan nasa ba.

Yakasai a wata hira ta wayar tarho da jaridar Vanguard a safiyar ranar Asabar, 27 ga watan Fabrairu, ya ce an tsare dan nasa ne tun daga ranar Juma’a lokacin da ya tafi gidan aski kuma yana kan hanyarsa ta komawa gida.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Asali: Legit.ng

Online view pixel