NNPP: Surukin Kwankwaso Ya Sha Kashi a Shari’ar Zaben Majalisa a Hannun APC

NNPP: Surukin Kwankwaso Ya Sha Kashi a Shari’ar Zaben Majalisa a Hannun APC

  • Nasiru Sule Garo ya rasa karar da ya kai kotun sauraron karar zabe, alkalai sun ba APC nasara
  • Jam’yyar adawa ta NNPP ta gagara karbe kujerar ‘dan majalisar tarayya mai wakiltar Kabo/Gwarzo
  • Flora Azinge ta zartar da hukunci cewa INEC ta yi daidai da ta ba Hon. Abdullahi Mu’azu nasara

Kano - Kotun da ke sauraron shari’ar zabukan majalisar tarayya da na dokoki da ke jiha, ta tabbatar da nasarar Abdullahi Mu’azu a zaben 2023.

Premium Times ta ce kotun da ke karbar korafin zaben 2023 ta ba Hon. Abdullahi Mu’azu da jam’iyyar APC gaskiya a shari’ar da aka gudanar.

Alkalan kotun sun ce jam’iyyar APC mai mulkin kasar ta lashe zaben majalisa a Kabo/Gwarzo.

Surukin Kwankwaso
Nasiru Sule Garo ya yi takara a NNPP Hoto: @nsgaro
Asali: Twitter

Nasiru Sule Garo (NNPP) bai dace ba

Nasiru Sule Garo ya shigar da karar ‘dan takara kuma ‘dan majalisa mai-ci, jam’iyyar APC da hukumar INEC a kan zaben da aka shirya a bana.

Kara karanta wannan

Sanatan APC Ya Lallasa Jam'iyyar PDP da LP, Kotun Zaɓen NASS Ta Yanke Hukunci

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Hon. Nasiru Garo bai gamsu da sakamakon da hukumar INEC ta ayyana ba, ya kalubalanci zaben amma rahoton ya ce bai samu nasara ba.

Alkalai sun ce ‘dan takaran jam’iyyar NNPP bai iya gamsar da su cewa an tafka kura-kurai a zaben kuma ba a bi abin da dokar zaben 2022 ta ce ba.

Lauyan ‘dan takaran NNPP ya yi ikirarin Mu’azu bai yi nasarar samun yawan kuri’un gaskiya da aka kada a zaben ba, an yi watsi da zancensa.

Daga cikin abubuwan da Garo ya fake da su shi ne an yi aringizo a akalla rumfunan zabe 20, ya kuma gabatar da shaidu 20 da ba a karba ba.

An ce ‘dan majalisar bai gabatar da takardun karatunsa a lokacin da ya yanki fam din shiga takara ba, alkalai sun yi fatali da wannan tuhuma.

Kara karanta wannan

Ahaf: Rashin Gaskiya Ta Sa Kotu Ta Tsige Dan Majalisar NNPP a Kano, An Ba Dan Takarar APC

Surukin Kwankwaso zai daukaka kara a NNPP?

Mai shari’a Flora Azinge da sauran alkalan ba su samu hujjojin da za su sa a rusa zaben ba a daidai lokacin da NNPP ta rasa wasu kujerunta.

Legit ba ta san matakin da tsohon ‘dan majalisar wakilan tarayyan kuma sabon Kwamishinan muhallin Kano zai dauka a game da batun ba.

‘Dan siyasar wanda ‘danuwa ne ga Murtala Sule Garo wanda ya nemi takarar mataimakin gwamna a APC a 2023 zai iya daukaka kara.

Rikicin Kwankwasiyya v NNPP

Dazu mu ka samu rahoto cewa wani Lauya ya ankarar da INEC cewa Rabiu Kwankwaso da mutanensa su na yi wa NNPP shisshigi

An bukaci hukumar INEC ta yi watsi da shirin ‘Yan Kwankwasiyya na canza dokoki da tambarin NNPP, da sunan ba su da ikon yin hakan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng