Duk da taron dangi sai da Kwankwaso ya kai Gwamnatin Ganduje kasa – Sule Garo
Dan majalisa mai wakiltan mazabar Gwarzo da Kabo a majalisar wakilan kasar, Nasiru Sule Garo ya bayyana cewa duk da taron dangin da aka yiwa Shugaban akidarsu ta Kwankwasiyya sai da maigidan nasu, Dr Rabiu Musa Kwankwaso ya kai Gwamnatin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje kasa.
A cewar Nasiru duk masu adawa da kyakyawar zuciya irin ta Kwankwaso toh sun makaoro domin a cewarsa tsohon gwamnan na jihar Kano yayi masu fintinkau.
A wata hira da yayi da jaridar Leadership Nasiru wanda ya fadi zaben dan majalisar wakilai wanda ya gudana a ranar Asabar, 23 ga watan Fabrairu yace shi baya bakin ciki ga faduwar da yayi a zabe domin cewarsa Allah ne mai bayar da mulki.
Yace: “Alhamdulillahi kamar kullum kuma kamar yadda aka sani ni ban shiga siyasa ko a mutu ko ayi rai ba, musamman ganin irin kaunar da al’ummar da nake wakilta ke yi min, wannan tasa sakamakon zaben da ya bayyana muka kalle shi tare da kyautatawa Allah zato, kuma daman cewa na yi Allah duk abin da yafi alhairi ya zaba mana. Muna kuma kyautata zato wannan bakaramin alhairi Allah ke nufi da matsayin sakamakon zabe ba.”
Yace babu wanda yayi wa jihar Kano irin hidimar da Kwankwaso yayi mata, kama daga gyara harkar ilimi, hanyoyi da sauransu.
KU KARANTA KUMA: Kujerar kakakin majalisa: Dogara ya ja baya daga tseren
An tattaro inda yake cewa: "Kwankwaso ne Gwamna daya tilo a Niaeriya da ya gina Jami’o’i biyu Jami’ar kimiya da fasaha dake Wudii da kuma North West, sai makarantu 24 da suka shafi harkokin inganta al’umma kai tsaye, ga kuma shirin nan na CRC wanda ake ciyar da daliban makarantun firamare tare da basu kayan makaranta kyauta, sai kuma tura ‘ya asalin Jihar Kano zuwa Kasashen waje domin karin ilmi tare da samun digiri har da digirgir a Jami’o’in cikin gida da waje."
SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng