"Da Yardar Allah Sai Na Kammala Wa’adin Mulkina a Raye", Gwamna Akeredolu Ya Koma Bakin Aiki

"Da Yardar Allah Sai Na Kammala Wa’adin Mulkina a Raye", Gwamna Akeredolu Ya Koma Bakin Aiki

  • Gwamna Rotimi Akeredolu na jihar Ondo ya koma bakin aiki bayan dogon hutu da ya tafi
  • Akeredolu ya ce da yardar Allah sai ya cika wa'adin mulkinsa kafin ya koma ga Allah
  • Gwamnan na APC dai ya shafe tsawon watanni uku baya kasar, inda ya tafi jinya a kasar Jamus

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Ondo - Gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, ya koma bakin aiki a hukumance bayan hutun jinya na watanni uku da ya tafi a kasar Jamus.

A ranar Alhamis, 7 ga watan Satumba ne Akeredolu ya dawo gida Najeriya daga Jamus inda ya shafe watanni uku yana jinya.

Rotimi Akeredolu ya koma bakin aiki
Da Yardar Allah Sai Na Kammala Wa’adin Mulkina a Raye, Gwamna Akeredolu Ya Koma Bakin Aiki Hoto: @thecableng
Asali: Twitter

Gwamnan ya samu tarba daga makusantansa a gidansa da ke Ibasan, babban birnin jihar Oyo.

Akeredolu ya koma bakin aiki bayan hutun jinya

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Gwamnan APC Da Ya Shafe Watanni Yana Jinya a Ƙasar Waje Ya Dawo Najeriya

A ranar Juma'a, Akeredolu ya gana da masu ruwa da tsaki daga jihar ciki harda Olamide Oladiji, kakakin majalisar dokoki na jihar, Lucky Aiyedatiwa, mataimakin gwamna da mambobin jam'iyyar All Progressives Congress (APC), a gidansa, rahoton The Cable.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A yayin ganawar, Akeredolu ya mika wasikarsa na komawa bakin aiki ga Oladiji sannan ya gabatar da kwafi ga Aiyedatiwa.

Gwamnan ya ce da izinin Allah, zai kasance a raye don kamma wa'adin mulkinsa, wanda zai kare a watan Fabrairun 2025.

A cikin wata sanarwa daga hadiminsa, Richard Olatunde, ya nakalto gwamnan yana cewa:

"Na dawo jiya kuma kamar yadda kuka sani, tafiya ce mai tsawo. Na yanke cewa dole sai na gana da ku a yau.
"Allah ya amsa addu'o'inmu, kuma godiya ta tabbata gare shi. Zan iya tabbatar maku cewa dawowarmu ni'ima ce ta Allah da addu'o'inku ne gaba daya, da na wadanda suke yi mana fatan alkhairi, ina mai godiya gareku sosai.

Kara karanta wannan

Gwamnan CBN, EFCC, Hafsun Soji da Mutanen Buhari da Tinubu Ya Kora a Kwana 100

"Allah ya yi abun da mafi akasarin mutanenmu suka so. Yawancin mutanenmu a nan sun duka sannan suka roki Allah ya dawo da mu, kuma mun dawo.
"Don haka, saboda sai da muka fara sauka a nan Ibadan, na ce sai na hadu da mambobin majalisar dokoki a nan.
"Ga mu a nan, kuma mun dawo. Na dawo, kuma da izinin Allah, zan kasance a raye don kammala wa'adin mulkina cikakke. Ina so na fada maku na dawo, kuma zan dawo bakin aiki nan take. Ga wasikar dawowa bakin aikina."

Ondo 2024: SSG ta ayyana shirinta na tsaya wa takarar gwamna

A wani labarin, mun ji cewa sakatariyar gwamnatin jihar Ondo, Princess Oladunni Odu, ta tabbatar da burinta na shiga tseren takarar gwamna a zaben jihar da ke tafe a shekara mai zuwa.

Princess Odu ta bayyana cewa ba abu ne mai wahala ba a samu mace a matsayin gwamnan jihar Ondo ba, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng