2023: Gwamnan APC Ya Ba Atiku, Obi Shawara ‘Su Guji Asarar Kudi’ a Kotun Koli

2023: Gwamnan APC Ya Ba Atiku, Obi Shawara ‘Su Guji Asarar Kudi’ a Kotun Koli

  • Yahaya Bello bai tunanin jam’iyyun PDP da LP za su iya yin galaba a kan Bola Tinubu a kotun koli
  • Kotun sauraron karar zabe ta ce jam’iyyar APC ta lashe zaben 2023, ta yi watsi da korafin ‘yan adawa
  • Gwamnan ya ji dadin nasarar Bola Ahmed Tinubu, ya ce APC za ta karbe kujerun Sanatocin jihar Kogi

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Kogi - Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya na ganin babu ta yadda kotun koli za ta rusa zaben 2023, ta tsige Bola Ahmed Tinubu.

Vanguard ta rahoto Yahaya Bello ya na mai ba Atiku Abubakar da Peter Obi shawarar su hakura da maganar daukaka karar zaben 2023.

Gwamnan ya na ganin ‘yan takaran jam’iyyun adawan ba za su kai ko ina ba ko sun daukaka kara a sakamakon rashin nasararsu a PEPT.

Kara karanta wannan

Mai Neman Karbe Kujerar NNPP Ya Kunyata, Alkali Ya Ce a Biya ‘Dan Majalisa N100, 000

Atiku Abubakar y
Atiku Abubakar zai je kotun koli Hoto: Atiku
Asali: Facebook

Shari'ar zaben 2023 ba ta kare ba

Kotun sauraron karar zabe ta yi watsi da karar PDP, LP da Allied Peoples Movement, APM. Lauyan Atiku Abubakar ya ce za su daukaka kara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake zantawa da manema labarai bayan ya ziyarci Kashim Shettima a fadar Aso Rock, Gwamna Bello ya samu tofa albarkacin bakinsa.

A cewar Bello, babu dalilin da zai sa Atiku Abubakar, Peter Obi da jam’iyyar APM su kalubalanci zaben shugaban kasa da aka yi a Fabrairu.

Gaskiyar APC ta fito a kotu

Premium Times ta rahoto Mai girma gwamnan ya ce sun yi murna da hukuncin da alkalan kotun karar zaben su ka yi, ya ce gaskiya tayi aiki.

Bello wanda yake shirin barin ofis a shekarar badi ya ce an dade a kotu kafin a yanke hukuncin da ya gaskata nasarar da INEC ta ba Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

Sharrin Shari'a: Sanatocin APC da Kotu Ta Kora Kafin a Cinye Albashin Wata 3 a Majalisa

"Babu abin da ya kai abin da ya kai samun nasara. Mu na farin ciki; ‘Yan Najeriya su na murna sannan gaskiya ta fito fili.
Mun yabawa duk abubuwan da su ka faru a jiya. Gaskiya ta bayyana. Alkalan sun zauna na kusan awanni 14 domin yin hukunci.

- Yahaya Bello

Baya ga shari’ar shugaban kasa, Alhaji Bello ya na sa rai APC ta karbe duka kujerun majalisar dattawan Kogi idan an daukaka kara.

NNPP ta doke APC a Kano

Alkalai sun tabbatar da nasarar Sagir Koki na jam’iyyar NNPP a kan ‘dan takaran APC, Muntari Ishaq Yakasai, a jiya aka samu rahoton.

Mai shari’a Flora Azinge tayi kaca-kaca da hujjoji da shaidun APC a karar zaben Majalisar Wakilan, su ka ce za su biya tarar N100, 000.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel