"Ni Dalibi Ne Mai Hazaka" Shugaba Tinubu Ya Bayyana Tarihin Karatunsa a Jami'a
- Shugaba Bola Tinubu ya bayyana tarihinsa na karatu a lokacin da yake jami'a, inda ya ce shi hazikin dalibi ne
- Yayin da yake jawabi ga ‘yan Najeriya mazauna Indiya, shugaban ya faɗi yadda Deloitte ya horar da shi sannan ya shiga kamfanin Exxon Mobil
- Tinubu ya je kasar Indiya ne domin halartar taron G-20, kuma ya gana da 'yan Najeriya wanda daliban Najeriya da ke karatu a kasar suka halarta
India - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa yana da kyakkyawan tarihi na hazaƙa a lokacin yana matsayin ɗalibin jami'a a ƙasar Amurka.
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa shugaba Tinubu ya bayyana haka ne yayin ganawarsa da 'yan Najeriya mazauna ƙasar Indiya ranar Alhamis, 7 ga watan Satumba.
Shugaba Tinubu ya yi jawabi ga 'yan Najeriya a Indiya
Hukuncin Kotu: An Bayyana Wani Muhimmin Dalili Da Zai Sanya Shugaba Tinubu Ya Cigaba Da Nasara Akan Atiku Da Peter Obi
A ranar Talata, 5 ga watan Satumba, 2023, Bola Tinubu ya bar fadar shugaban ƙasa da ke Abuja zuwa New Delhi a Indiya, inda aka gayyace shi taron shugabannin ƙasashen G-20.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Vanguard ta ce a wata sanarwa da kakakin shugaban ƙasa, Ajuri Ngelale, ya fitar ya bayyana cewa taron ya samu halartar ɗaliban Najeriya da ke karatu a ƙasar Indiya.
Shugaba Tinubu ya bayyana kwarin guiwar cewa ɗaliban zasu cimma nasara a karatun da suke yi daban-daban idan suka sa gaskiya da sadaukarwa.
Tinubu ya faɗi yadda ya fara aiki da Exxon Mobil
Sanarwan ta tattaro cewa shugaban ƙasa ya yi farin ciki da haɗuwa da 'yan Najeriya mazauna Indiya, inda ya ce iliminsa ne ya kai shi matsayin da ya taka yanzu.
"Na fara da ƙarami, ni mai gadi ne, ina koyar da ɗalibai a makaranta, ni ɗalibi ne mai hazaƙa. Na shiga Deloitte kuma ɗaya daga cikin manyan kamfanonin lissafin kuɗi a duniya ya horar da ni saboda karatuna."
Tinubu ya ƙara da cewa ya tambayi kamfanin ko suna da rassa a Najeriya, sai suka shaida masa cewa suna da abokan hulda da yawa a kasarsa da za su iya daukarsa aiki.
Daga nan ya bayyana cewa a haka ya shiga kamfanin Exxon Mobil kuma saboda nasarar da ya samu a muƙaman babban Odita Janar, Ma’aji da Akanta.
Gwamnan APC Da Ya Shafe Watanni Yana Jinya a Ƙasar Waje Ya Dawo Najeriya
A wani rahoton na daban Gwamna Rotimi Akeredolu na jihar Ondo ya dawo gida Najeriya daga ƙasar Jamus inda ya shafe dogon lokacin yana jinya.
Gwamna Akeredolu ya bar Najeriya zuwa ƙasar Jamus watanni da dama da suka gabata domin jinyar rashin lafiyar da yake fama da ita.
Asali: Legit.ng