"Ku Amince da Hukuncin Ƙotu" Sanata Akpabio Ya Shawarci Atiku da Obi

"Ku Amince da Hukuncin Ƙotu" Sanata Akpabio Ya Shawarci Atiku da Obi

  • Sanata Godswill Akpabio ya yi kira ga yan adawa da su rungumi hukuncin da kotun zabe ta yanke wanda ya tabbatar sa nasarar Bola Ahmed Tinubu a zaben 2023
  • Shugaban Majalisar Dattawan ya bayyana cewa hukuncin ya kara tabbatar da abinda yan Najeriya suka zaba da wadanda nauyi ya hau kansu
  • Haka zalika Akpabio ya kara da cewa an samu ci gaba sosai a tsarin gudanar da zaben Najeriya wanda ke bukatar goyon baya daga kowane bangare

FCT Abuja - Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Godswill Akpabio, ya roƙi 'yan adawa su rungumi ƙaddara, su amince da hukuncin da Kotun sauraron kararrakin zaɓen shugaban ƙasa ta yanke.

A ranar Laraba (Jiya) 6 ga watan Satumba, 2023, Kotun zaɓe ta tabbatar da nasarar shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 25 ga watan Fabrairu, 2023, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Bola Tinubu Ya Yi Magana Daga Indiya Mintuna da Doke PDP da LP a Kotu

Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio.
"Ku Amince da Hukuncin Ƙotu" Sanata Akpabio Ya Shawarci Atiku da Obi Hoto: Godswill Akpabio
Asali: Facebook

Kwamitin Alƙalai 5 karkashin mai shari'a Haruna Tsammani ya yi fatali da ƙararrakin Atiku Abubakar na PDP, Peter Obi na LP da Chichi Ojei na jam'iyyar APM.

A wata sanarwa da ofishin mai magana da yawunsa ya fitar, Sanata Akpabio ya ayyana hukuncin kotun da tabbatar da muradin 'yan Najeriya ga tikitin Tinubu/Shettima.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya yi nuni da cewa, kotun ta yi nazari sosai kan dukkan ƙorafe-ƙorafen da masu shigar da kara suka gabatar kana ta yanke hukunci karara kan sahihancin tsarin zaben Najeriya.

An samu ci gaba a tsarin zabe inji Akpabio

Shugaban Majalisar Dattawan ya ce duk da kalubalen da ake fuskanta, tsarin zaben Najeriya na samun ci gaba kuma ya cancanci yabo da goyon bayan duka 'yan Najeriya da ƙawayen ƙasar nan.

Bisa haka,Sanata Akpabio ya roki Atiku da Peter Obi da sauran yan Najeriya baki daya su mara wa gwamnatin Bola Tinubu baya yayin da take kokarin tabbatar da kudirin jam'iyyar APC na sabunta fata.

Kara karanta wannan

Buhari Ya Yi Farin Ciki, Ya Yi Magana a Kan Nasarar Tinubu a Kotun Zaben 2023

A ruwayar The Nation, Akpabio ya ce:

"Na yaba da hukuncin Kotun zabe inda ta tabbatar da nasarar mai girma shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima a babban zaben 2023 da ya gabata. Haka nan ina taya jam'iyyar mu ta APC murna bisa nasarar da ta samu a Kotu."
"Wannan hukunci ya kara jaddada muradin yan Najeriya da amintar da suka yi wa dan takarar shugaban kasa da mataimakinsa a zaben watan Fabrairu, 2023.''
"Yayin da Kotu ta share duk wata tantama a korafe-korafen da masu shigar da kara suka gabatar, ina rokon duk wani mai kishin kasa ya amince da hukuncin kana ya hada hannu da gwamnatin Tinubu a kokarinta na ceto da inganta rayuwar 'yan Najeriya."

Jerin Alkalan Kotun Koli Da Za Su Yanke Hukunci A Karshe Bayan Sanin Sakamakon Kotu A Jiya

A wani labarin na daban kuma mun tattaro muku jerin Alkalan Kotun Koli da zasu yanke hukuncin karshe kan sahihancin zaben shugaban kasa na 2023.

Kara karanta wannan

Dandazon Mutane Sun Yi Zanga-Zanga a Kotun Zaɓe, Sun Aike da Muhimmin Saƙo Ga Atiku da Obi

Bayan hukuncin kotun sauraran kararrakin zaben shugaban kasa, jam'iyyar PDP da Labour sun kudiri aniyar daukaka kara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel