Hukuncin Kotun Zabe: Shettima Ya Yi Wa Atiku Wankin Babban Bargo, Ya Ce Zai Siya Masa Kaji Da Akuyoyin Kiwo
- Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya ce zai yi wa Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP ritaya, zuwa gidan kiwon dabbobi
- Shettima ya yi martanin ne yayin zantawa da manema labarai a wajen kotun daukaka kara a Abuja, jim kadan bayan kotun zabe ta tabbatar da nasarar Shugaban kasa Bola Tinubu
- Atiku ya yi takarar kujerar shugaban kasar Najeriya sau shida a 1993, 2007, 2011, 2015, 2019, da 2023 ba tare da nasara ba
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Abuja - Mataimakin shugaban kasar Najeriya, Kashim Shettima, ya ce jam'iyyar All Progressives Congress (APC) za ta yi wa Atiku Abubakar ritaya zuwa Kombina inda zai iya shafe rayuwarsa yana kiwon akuyoyi, kaji masu kwai da kajin turawa.
Shettima na martani ne ga nasarar da suka samu a kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa a ranar Laraba, 6 ga watan Satumba.
Zan yi wa Atiku ritaya zuwa gidan kiwon kaji, Shettima
Tsohon gwamnan na jihar Borno ya bayyana cewa Dubai wanda ita ake kallo a matsayin kasar dan takarar shugaban kasar na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ya fi so ba zai zama wajen ritayarsa ba.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Jaridar The Cable ta nakalto Shettima yana cewa:
"Ba za mu yi wa Atiku Abubakar ritaya zuwa Dubai ko Morocco ba. Zan yi masa ritaya zuwa Kombina, zan siya masa akuyoyi da kajin turawa da kaji masu kwai don ya shafe rayuwarsa yana kiwon akuyoyi da kajin turawa."
Shettima ya yi kira ga Atiku da Obi su zo ayi da su
Bugu da kario, Shettima ya yi kira ga Atiku, Labour Party (LP), Peter Obi da Allied Peoples Movement (APM) da su hada hannu da gwamnatin Bola Tinubu wajen gina sabuwar Najeriya.
Kalamansa:
"A madadin ubangidana, ina mai kira ga Wazirin Adamawa, Atiku Abubakar, da Mista Peter Obi, abokina na kwarai, da su hana hannu don gina sabuwar Najeriya."
Ganduje ya bukaci hadin kai daga Atiku, Peter Obi bayan yanke hukuncin kotu
A wani labarin, shugaban jam'iyyar APC, Dakta Abdullahi Ganduje ya bukaci hadin kai bayan yanke hukuncin zaben shugaban kasa.
Ganduje ya kirayi jam'iyyun PDP da Labour da su goyi bayan Shugaba Tinubu wurin inganta rayuwar al'umma.
Asali: Legit.ng