Ganduje Ya Bukaci Hadin Kai Daga Atiku, Peter Obi Bayan Yanke Hukuncin Kotu
- Dakta Abdullahi Umar Ganduje, shugaban jam'iyyar APC ya nemi hadin kan 'yan jam'iyyun adawar PDP da Labour don ciyar da kasa gaba
- Ganduje ya bayyana haka ne a jiya Laraba 6 ga watan Satumba a Abuja inda ya yabi bangaren shari'a a hukuncin da su ka yi
- Shugaban jam'iyyar ya ce bangaren shari'ar kasar sun yi abin a yaba yadda su ka yanke hukunci ba tare da son kai ko tsoro na
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
FCT, Abuja - Shugaban jam'iyyar APC, Dakta Abdullahi Ganduje ya bukaci hadin kai bayan yanke hukuncin zaben shugaban kasa.
Ganduje ya kirayi jam'iyyun PDP da Labour da su goyi bayan Shugaba Tinubu wurin inganta rayuwar al'umma.
Meye Ganduje ke bukata daga Atiku, Obi?
Ganduje ya bayyana haka a cikin wata sanarwa a jiya Laraba 6 ga watan Satumba a Abuja, PM News ta tattaro.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ya ce tabbas wannan hukunci ya kore dukkan korafe-korafen da masu shigar da kara su ka yi.
Ya ce:
"Ina kiran 'yan adawa da su amince da hukuncin kotu.
"Akwai lokutan zabe da dama a gaba, 'yan takara za su iya gwada sanuwarsu ga a zabe."
Ganduje ya bayyana matsayarsa kan hukuncin
Ganduje ya bayyana wannan hukunci a matsayin nasara ga 'yan Najeriya inda ya ce gwamnatinsu za ta cika alkawuran da ta dauka.
Shugaban APC ya ce tsayawa da 'yan takarar su ka yi a kotu ya nuna yadda su ka yarda da kotunan zaben kasar, cewar Vanguard.
Ya kara da cewa:
"Tun farko ina da tabbacin nasarar shugaban kasa a wannan shari'ar.
"Ina taya bangaren shari'a murna yadda su ka gudanar da shari'ar ba tare da tsoro ko nuna son kai ba."
Ganduje Ya Yi Alkawarin Aiki Tukuru Ga APC
A wani labarin, sabon shugaban jam’iyyar APC mai mulki, Abdullahi Ganduje ya yi alkawarin daidaita al’amura a jam’iyyar don tabbatar da nasara a zabukan jihohi da ke tafe.
A ranar 11 ga watan Nuwamba ne ake sa ran za a yi zabukan jihohin Imo da Kogi da Bayelsa.
Wannan na zuwa ne bayan jam'iyyar APC ta zabe shi a matsayin shugabanta na kasa.
Asali: Legit.ng