Ta Leko ta Koma: Jam'iyyar LP ta Rasa ‘Yan Majalisa 3 a Kotu a Cikin Kwanaki 100
- Nkiruka Onyejeocha za ta iya komawa majalisa a sakamakon doke Hon. Amobi Ogah a kotun zabe
- Hon. Ndudi Elumelu ya yi galaba a kan Ngozi Okolie domin ba ta da rajista a LP a lokacin zaben 2023
- A Legas, Seyi Sowunmi ya karbe kujerarsa bayan ‘dan jam’iyyar LP ya shafe watanni 3 a Majalisa
Abuja - A watan Fabrairu aka gudanar da zaben ‘yan majalisar tarayya, jam’iyyar LP ta bada mamaki musamman a kudu maso gabashin kasar.
Jam’iyyar hamayyar ta lashe kujerun majalisar wakilai fiye da 20 a bana, amma sannu a hankali kotu ta na gwagwuye mata ‘yan majalisa.
Rahoton nan ya tattaro jerin wasu ‘yan majalisar tarayya a karkashin LP da kotu ta karbe kujerarsu:
1. Hon Amobi Ogah (LP)
Karar da Hon Nkiruka Onyejeocha ta shigar a game da zaben mazabar Isuikwuato/Umunneochi a Abia ya jawo aka rusa nasarar Hon Amobi Ogah.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Kotun korafin zabe ta ce Ogah bai cancanci ya je majalisa ba domin kara mai lamba EPT/AB/HR/8/2023 ya tabbatar da shi ba ‘dan jam’iyyar LP ba ne.
A dokar zabe da tsarin mulki, dole jam’iyyar siyasa ce za ta dauki dawainiyar ‘dan takara har ya iya samun mukami, LP ba ta bi wannan ka’ida a nan ba.
2. Hon. Ngozi Okolie (LP)
Kotu ta zartar da hukunci inda ta tsige Honarabul Ngozi Okolie daga matsayin mai wakiltar mazabar Aniocha/Oshimili a majalisar wakilan tarayya.
Abin da kotu ta zartar a EPT/DL/HR/06/2023 shi ne a nan ma an sabawa doka wajen tsaida ‘dan takaran LP, an bada tikiti ga wanda ba ‘dan jam’iyya ba.
Wanda alkalai su ka ba kujerar shi ne Ndudi Elumelu duk da kuri’u 33, 466 ya samu a karkashin PDP, ya zo bayan LP da mutane 53, 879 su ka zabe ta.
3. Seyi Sowunmi (LP)
Kujerar ‘dan majalisa na shiyyar Ojo a Legas ta na cikin wadanda ta kubucewa LP bayan nasarar da ‘dan takararta ya samu har aka rantsar da shi.
Kwanaki aka ji Hon. Lanre Ogunyemi ya yi nasara a kotun sauraron karar zabe, aka ce ‘dan takaran na APC ne asalin wanda ya dace da mukamin.
A wannan karo ma, Alkalan kotun karar zabe sun tabbatar da Seyi Sowunmi bai cancanci shiga zabe ba saboda haka aka yi watsi da kuri’unsa.
4. Sunday Nnamchi
Farfesa Sunday Nnamchi ya na daf da rasa kujerar da yake kai ta ‘dan majalisa mai wakiltar Enugu ta Gabas da Isi-Uzo a majalisar wakilan tarayya.
Hon. Prince Nnaji ya shigar da kara a kotun zabe kuma ya yi nasara. Alkalai sun tabbatar da Nnamchi bai da hurumin shiga takara a inuwar LP.
Asali: Legit.ng