Tsohon Sanata Ya Caccaki Atiku Kan Kalubalantar Nasarar Shugaba Tinubu

Tsohon Sanata Ya Caccaki Atiku Kan Kalubalantar Nasarar Shugaba Tinubu

  • An buƙaci ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya daina ƙalubalantar nasarar Shugaba Tinubu
  • Tsohon sanata, Soji Akanbi, ya bayyana cewa bai kamata Atiku ya manta da abokantaka da ƴan uwantakar da ke tsakaninsa da Shugaba Tinubu ba
  • Akanbi ya yi nuni da yadda Atiku ya ruga wajen Tinubu bayan sun samu saɓani da tsohon shugaban ƙasa Obasanjo a PDP

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Oyo - Tsohon sanatan Oyo ta Kudu, Rilwan Soji Akanbi ya caccaki ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) Atiku Abubakar kan ƙalubalantar nasarar shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.

Akanbi ya ce Atiku, wanda ya abotarsa da Tinubu ta kai shekara 31 tun shekarar 1992, ya watsar da abin da ke tsakaninsu saboda ya faɗi zaɓe.

Kara karanta wannan

Bayan Juyin Mulkin Gabon, Shugaba Tinubu Ya Faɗi Ainihin Abinda Yake Jin Tsoron Ya Faru

Tsohon sanata ya caccaki Atiku Abubakar
Sanata Akanbi ya caccaki Atiku Abubakar Hoto: Bola Ahmed Tinubu/Atiku Abubakar
Asali: Facebook
"Amma wannan shi ne Atikun da ya ke bi lungu da saƙo yana neman wani ɗan guntun abu da zai ɓata nasarar shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, babban abokinsa a baya." A cewarsa.

Menene dalilin jin zafin?

A wata sanarwa wacce Legit.ng ta samu, tsohon sanatan ya tuna yadda Atiku ya je wajen Tinubu domin ya taimaka masa a siyasarsa bayan ya yi rashin nasara a hannun marigayi tsohon shugaban ƙasa Umaru Musa Yar'adua.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Akanbi ya bayyana cewa Tinubu shi ne ya ceto Atiku daga muzgunawar da tsohon shugaban ƙasa Obasanjo ya ke yi masa.

A kalamansa:

"Za a iya tunawa cewa, lokacin da Atiku ya sha kashi a jam'iyyar PDP, sannan ya faɗi zaɓen fidda gwanin shugaban ƙasa a hannun marigayi Alhaji Musa Yar'adua, abokinsa Tinubu shi ne ya ceto shi ya ba shi jam'iyyar da zai yi takara."

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu Ya Maida Martani Kan Sabon Juyin Mulkin da Sojoji Suka Yi a Gabon, Ya Faɗi Mataki Na Gaba

"Haka nan za a iya tuna yadda Tinubu ya ceto Alhaji A. Atiku daga hannun tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo wanda ya shirya soya shi kamar naman akuya, kamar yadda Tinubun ya tabbatar da kansa a wajen yaƙin neman zaɓen APC."

Ya shawarci Atiku da kada ya ci moriyar ganga ya gada korenta domin ba a san abin da gobe za ta yi ba.

Akanbi ya yi mamakin yadda idon Atiku ya kulle ya manta da abokantakarsa da Shugaba Tinubu, inda ya cigaba da ƙalubalantar nasarar abokinsa.

Gwamnan Katsina Ya Raba N20m

A wani labarin kuma, gwamnan jihar Katsina ya raba N20m iyalan ƴan sakai da suka rasa ransu a bakin aiki.

Gwamna Dikko Umaru Radda ya raba kuɗin ne ga iyalan ƴan sakai 33 da suka rasa ransu a bakin aiki a faɗin jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng