Tinubu, Ganduje, Obaseki da Gwamnoni 10 da Su ka Yi Rigima da Mataimakansu a Siyasa
- A yanzu babu jituwa tsakanin Mai girma Godwin Obaseki na jihar Edo da mataimakin gwamna
- A mabanbantan rahoto, rigimar gwamnan da mataimakinsa watau Philip Shaibu ta fito fili a Edo
- Sai dai ba su ne farau ba, an yi gwamnonin da su ka yaki mataimakansu, har aka tunbuke wasunsu
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Edo - Rahoton nan wanda Punch ta fitar ya kawo jerin gwamnonin jihohin da su ka takawa mataimakansu burki, kamar yadda Obaseki yake neman yi.
1. Bola Tinubu vs Femi Pedro
A lokacin Bola Tinubu ya na gwamnan Legas, ya yi rigima da mataimakinsa Otunba Olufemi Pedro saboda ya goyi bayan Tunde Fashola SAN ya gaje shi.
Kofoworola Akerele ta yi wa Tinubu mataimakin gwamna a jihar Legas tsakanin 1999 da 2003.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
2. Rochas Okorocha vs Jude Agbaso & Eze Madumere
Rahoton ya ce shi ma Rochas Okorocha ya samu sabani da mataimakan gwamna biyu da ya ke mulki. An fara ne da tsige Jude Agbaso a majalisa a 2013.
Bayan an nada Prince Eze Madumere, sai su ka yi rigima da mai gidansa da aka zo takarar sabon gwamna, Okrocha ya goyi bayan surukinsa ya gaje shi a Imo.
3. Abdullahi Ganduje vs Hafiz Abubakar
A Agustan 2018 ne Farfesa Hafiz Abubakar ya ajiye mukaminsa na mataimakin gwamna a Kano da sabani ya yi yawa tsakaninsa da Abdullahi Ganduje.
Abdullahi Ganduje ya musanya zargin maye gurbin Farfesan da yake tare da Rabiu Musa Kwankwaso a lokacin da Nasiru Gawuna kafin ayi zaben 2019.
4. Obong Victor Attah vs Chris Ekpenyong
A Akwa Ibom, Obong Victor Attah bai samu jituwa sosai da Dr. Chris Ekpenyong ba. Rigimar gwamnan da mataimakinsa ta jawo majalisa ta tsige Ekpeyong.
5. Ayodele Fayose vs Abiodun Aluko
Ana zargin a lokacin da Ayo Fayose ya ke gwamna a jihar Ekiti, shi ya yi silar korar mataimakinsa Abiodun Aluko bayan majalisa ta same shi da laifuffuka 16.
6. Isa Yuguda vs Garba Gadi
A lokacin da Alhaji Garba Gadi ya ki sauya-sheka daga ANPP zuwa PDP wannan ya haddasa rigima a Bauchi, har ta kai Isa Yuguda ya jawo an tunbuke shi.
7. Olusegun Mimiko vs Ali Olanusi
A maimakon ya sauya-sheka zuwa PDP, sai Alhaji Ali Olanusi ya koma APC, hakan ya fusanta mai gidansa Olusegun Mimiko, hakan ya jawo ya rasa kujerarsa.
8. Yahaya Bello vs Simon Elder Achuba
Simon Elder Achuba ya samu sabani da Gwamna Yahaya Bello a Kogi, daga baya an ji yadda aka tunbuke shi bayan wani bincike da ya zo gaban Alkalin Alkalai.
9. Alfred Agboola Ajayi vs Rotimi Akeredolu
Tsakanin 2017 da 2021, Alfred Agboola Ajayi ne mataimakin gwamnan Ondo, daga baya ya yi rigima da Rotimi Akeredolu har ya nemi takara da uban gidansa.
“Kwankwaso Na Ta Kamun Kafa Don Ya Zama Ministan Abuja a Gwamnatin Tinubu”: Ganduje Ya Yi Zargi a Bidiyo
10. Bello Matawalle vs Mahadi Gusau
A lokacin da Bello Matawalle ya tafi APC, Mahadi Gusau bai bar PDP ba wanda hakan ya yi sanadiyyar tsige shi, bayan sun bar ofis, sai kotu ta ba shi gaskiya.
Ana kan kokarin maido APC a Kano
Saboda a samu nasara a kotu zabe ne aka ji labari mukarraban Gwamnati da Rabi’u Musa Kwankwaso su ka fito salla ta musamman a jihar Kano.
Idan NNPP ta yi rashin sa’a, za a iya yin waje da Gwamna Abba Kabir Yusuf da bayan watanni uku a kan mulki, hakan zai iya ba kowa mamaki a kasar.
Asali: Legit.ng