Ganduje na gana min azaba – Mataimakin Gwamnan Kano

Ganduje na gana min azaba – Mataimakin Gwamnan Kano

Mataimakin gwamnan jihar Kano Farfesa Hafiz Abubakar ya yi zargin cewa Gwamnan jihar Dr. Abdullahi Umar Ganduje na azabtar da shi.

A cewar Hafiz sama da shekara biyu kenan da gwamnatin Ganduje ke nuna masa wariya tare da tauye masa hakkokinsa, saboda yana biyayya ga Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso.

Mataimakin gwamnan ya bayyana cewa rayuwarsa na cikin hatsari, yana mai bada misali da abinda ya faru ga wani jami'in gwamnatin Kano Dr. Bala Muhammad a 1981, inda aka bi shi har gida aka kashe shi, yayin wata zanga-zangar kin jinin gwamnatin Abubakar Rimi.

Mataimakin na gwamnan Kano ya ce da kudinsa ya ke yi wa gwamnatin Kano duk wata hidima da ya ke yi mata.

Ganduje na gana min azaba – Mataimakin Gwamnan Kano

Ganduje na gana min azaba – Mataimakin Gwamnan Kano

Ya yi zargin cewa duk abinda ake yi masa ana yi masa saboda alakarsa da Kwankwaso.

Ya ce kawo yanzu yana nan a cikin jam'iyyar APC kuma har yanzu shi ne mataimakin gwamnan jihar Kano.

KU KARANTA KUMA: Babu zaman lafiya a majalisar dattawa har sai Saraki yayi murabus - Sanata

To amma fa ya ce ya daure kayansa domin ficewa daga jam'iyyar ta APC idan lokaci ya yi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel