Buba Galadima Ya Yi Magana Kan Batun Dakatar Da Kwankwaso Daga Jam'iyyar NNPP

Buba Galadima Ya Yi Magana Kan Batun Dakatar Da Kwankwaso Daga Jam'iyyar NNPP

  • Jigon jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP), Buba Galadima, ya yi magana kan batun dakatar da Rabiu Musa Kwankwaso daga jam'iyyar
  • Buba ya bayyana dakatar da.jagoran jam'iyyar na ƙasa a matsayin irin barkwancin da ake yi a finafinan Nollywood da Hollywood
  • Jigon ya bayyana cewa waɗanda su ke iƙirarin korar Kwankwaso daga jam'iyyar tuni aka daɗe da korar su daga cikinta

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - Alhaji Buba Galadima ya yi magana kan rikicin da ya dabaibaye jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP).

Buba Galadima wanda yana ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa jam'iyyar ya bayyana batun dakatar da Rabiu Musa Kwankwaso daga jam'iyyar a matsayin wasan kwaikwayo.

Buba Galadima ya yi magana kan dakatar da Kwankwaso
Buba Galadima tare da Rabiu Musa Kwankwaso Hoto: @KwankwasoRM
Asali: Twitter

Jigon na jam'iyyar NNPP a yayin wata tattaunawa da Channels tv a shirinsu na Politics Today, ranar Talata da daddare, ya haƙiƙance cewa babu wani ruɗani a cikin jam'iyyar.

Kara karanta wannan

Ana Dakon Hukuncin Kotu Kan Zaben Abba, Dan Takarar Gwamna Ya Sauya Sheka Zuwa APC a Kano

Wata ƙungiya dai a cikin jam'iyyar ta dakatar da Kwankwaso wanda ya yi takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar bisa zargin cin dunduniyar jam'iyyar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Buba ya kare Kwankwaso

Sai dai, Galadima ya yi fatali da zarge-zargen da su ke yi akan Kwankwaso.

"Lokacin da na ga labarin a soshiyal midiya, na ɗauka irin barkwancin nan ne na finafinan Nollywood da Hollywood." A cewarsa.

Ya bayyana cewa ƴan tsirarun shugabannin waɗanda da suka yi iƙirarin dakatar da Kwankwaso, an kore su daga jam'iyyar NNPP.

"Bari na fayyace yadda abun yake, waɗanda aka kora su ne Boniface Okechukwu Aniebonam da Gabriel Agbor Major." A cewarsa.
"Dukkaninsu da aka kora sai da aka kirasu gaban kwamitin ladabtarwa. An titsiyesu da tambayoyi inda suka amsa zunaban da suka aikata, sannan a bisa amsa laifin da suka yi ne aka ba kwamitin gudanarwa na ƙasa shawarar ya kore su."

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC Ta Yi Amai Ta Lashe Kan Yan Tawagar Yakin Neman Zabenta, Ta Bayyana Gaskiyar Zance

Shugaban NNPP Ya Magantu Kan Dakatar Da Kwankwaso

A wani labarin kuma, shugaban jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) na jihar Kano, ya musanta cewa jam'iyyar ta dakatar da Rabiu Musa Kwankwaso.

Hashimi Dunguruwa ya bayyana cewa batun dakatarwar da aka ce an yi wa ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar, kanzon kurege ne kawai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng