Ana Dakon Hukuncin Kotu Kan Zaben Abba, Dan Takarar Gwamna Ya Sauya Sheka Zuwa APC a Kano

Ana Dakon Hukuncin Kotu Kan Zaben Abba, Dan Takarar Gwamna Ya Sauya Sheka Zuwa APC a Kano

  • Dan takarar gwamnan Kano a jam'iyyar PRP, Salihu Tanko Yakasai, ya fice daga jam'iyyar
  • Yakasai ya sanar da komawarsa tsohuwar jam'iyyarsa ta All Progressives Congress (APC)
  • Wannan na kunshe ne a cikin sanarwar da ya fitar a shafinsa na soshiyal midiya a ranar Laraba, 30 ga watan Agusta

Dan takarar gwamnan jihar Kano na jam'iyyar PRP a zaben 2023, Salihu Tanko Yakasai, ya sauya sheka zuwa jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

Yakasai ya sanar da komawarsa tsohuwar jam'iyyarsa a cikin wata wallafa da ya yi a shafinsa na manhajar X a ranar, 30 ga watan Agusta.

Salihu Tanko Yakasai ya koma Kano
Ana Dakon Hukuncin Kotu Kan Zaben Abba, Dan Takarar Gwamna Ya Sauya Sheka Zuwa APC a Kano Hoto: @dawisu
Asali: Twitter

"Ganduje ya nemi na dawo APC kuma na amsa kira", Yakasai

Kafin sauya shekarsa daga APC gabannin babban zaben 2023, Yakasai ya kasance hadimin tsohon gwamnan jihar Kano kuma shugaban jam'iyyar APC na kasa mai ci a yanzu, Abdullahi Umar Ganduje.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Jam'iyyar APC Ta Kara Haddasa Ruɗani a PDP Kan Ministan Shugaba Tinubu

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya kuma bayyana cewa tsohon ubangidan nasa ne ya yi masa tayin dawowa cikinsu domin a ci gaba da tafiya a tare.

Ya rubuta a shafin nasa:

"Shugaban jam'iyyar APC na kasa, mai girma Dr Abdullahi Umar Ganduje OFR, ya nemi na dawo jam'iyyar APC sannan na ci gaba da bayar da gudunmawana wajen ciyar da jam'iyyar gaba, wanda tuni na amsa tayin da hannu bibbiyu. Na janye katin shaidar kasancewa dan jam'iyyar PRP sannan na sake komawa jam'iyyar APC."

Jama'a sun yi martani kan ficewar Yakasai daga PRP zuwa APC

@yakubwudil ya yi martani:

"Allah yasa hakan ya zama alkhairi gare ka da Kano gaba ɗaya, boss."

@ahmadciese ya ce:

"Barka da dawowa."

@Khalifa_Emgeear ya yi martani:

"Dama babu inda yaje "

@RIbyash ya ce:

"Kada ka gwada hakan yallabai.

Kara karanta wannan

“Kwankwaso Na Ta Kamun Kafa Don Ya Zama Ministan Abuja a Gwamnatin Tinubu”: Ganduje Ya Yi Zargi a Bidiyo

"Shigo shigo ba zurfi zasuyi maka."

@_Ahmadidris:

"Allah ya taimaka sir."

@al_shekarau_:

"Allah yasa hakan shine mafi alkhairi."

Alamu sun nuna Abba ya karaya a shari’ar zaben gwamna - Yakasai

A gefe guda, mun ji cewa ana shari’a gaban alkalai a kotun sauraron karar zaben gwamnan jihar Kano, Salihu Tanko Yakasai ya tofa albarkacin bakinsa.

Alhaji Salihu Tanko Yakasai wanda ya yi takarar gwamna a zaben 2023 a karkashin jam’iyyar SDP, ya bayyana kuskuren da NNPP ta yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel