Siyasar Kano: Jam’iyyar NNPP Ta Kara Samun Karin Kujerun Majalisar Dokoki da Tarayya

Siyasar Kano: Jam’iyyar NNPP Ta Kara Samun Karin Kujerun Majalisar Dokoki da Tarayya

  • Murtala Muhammad Kadage shi ne zababben ‘dan majalisar yankin Garko a jihar Kano
  • Alamu na nuna Aminu Sa'adu Ungogo yana cikin ‘yan majalisar da za a rantsar a NNPP
  • Muhammad Bello Shehu ya doke Hon. Aminu Sulaiman Goro da Shuaibu Abubakar a Fagge

Kano - Murtala Muhammad Kadage da ya tsaya takara a NNPP ne wanda aka sanar a matsayin zababben ‘dan majalisar Garko a jihar Kano.

A yammacin yau Daily Trust ta rahoto cewa Honarabul Murtala Muhammad Kadage ya yi nasara a kan ‘dan takaran APC, Mal. Abba Ibrahim.

Nasarar ta yau ta na nufin jam’iyyar NNPP ta samu karin kujera a majalisar dokokin Kano.

Jaridar ta ce Baturen zaben hukumar INEC, Farfesa Suleiman Mudi na jami’ar Bayero da ke Kano ya sanar da cewa NNPP ta zo ta daya a zaben.

Kara karanta wannan

Cikon Zaɓe: Jam'iyyar APC Ta Ƙara Lashe Zaben Sanata a Arewacin Najeriya

Mazabun Garko, Ungogo...

A madadin hukumar INEC, malamin jami’ar ya mika godiya ta musamman ga mutanen karamar hukumar Garko da suka bada hadin-kai.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Legit.ng Hausa ta fahimci Aminu Sa'adu Ungogo ya kama hanyar zama ‘dan majalisar jiha, zai wakilci mazabar Ungogo a karkashin NNPP.

NNPP.
Magoya bayan Jam’iyyar NNPP Hoto: @SaifullahiHon
Asali: Facebook

Farfesa Tijjani Hassan Darma ya tabbatar da jam’iyyar NNPP ta doke APC da ratar kusan 6,000. An sake zaben ne a rumfuna goma da ke yankin.

A mazabar Gabasawa, baturen zaben ya ce Muhammad Danzumi Salisu ya samu kuri’u 15, 806, sai Nuhu Zakariyya Abdullahi ya samu 17, 761.

Kamar yadda muka samu labari, NNPP ta zo ta farko sai APC, shi kuma ‘Dan takarar jam’iyyar PDP watau Isa Husaini ya zo na uku da kuri’u 5, 114.

APC ta zo ta uku a Fagge

Daily Trust ta ce a majalisar wakilan tarayya, Barista Muhammad Bello Shehu na NNPP ne aka sanar a matsayin wanda zai wakilci mazabar Fagge.

Kara karanta wannan

Zaben yau Asabar: Mata sun tona asirin APC a jihar Arewa, sun fadi yadda ake ba su kudi

Yayin da APC ta rike kujerar Tudun Wada da Doguwa, jam’iyyar hamayyar tayi nasara a Fagge. Farfesa Ibrahim Tajo Suraj ya ce APC ta zo ta uku.

Za a karasa zaben 2023

A zaben yau ne aka ji labari za a san su wanene za su zama Sanatocin jihar Sokoto da kuma na Zamfara ta tsakiya, da kuma wasu 'yan majalisa a Kano.

Jam’iyyun APC da PDP su na tseren karbe gidan Gwamnati a Jihohin Adamawa da Kebbi, jama'a sun zura kunnawa domin jin yadda zaben zai kasance.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel