Ministocin Tinubu: An Bayyana Wanda Shugaba Tinubu Yakamata Ya Ba Ministan Matasa

Ministocin Tinubu: An Bayyana Wanda Shugaba Tinubu Yakamata Ya Ba Ministan Matasa

  • An bayyanawa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu wanda yakamata ya naɗa muƙamin ministan matasa a gwamnatinsa
  • Wata gamayyar wasu ƙungiyoyi sun buƙaci shugaban ƙasar ya naɗa Alhaji Yerima Shettima ministan matasa
  • Shugabannin ƙungiyoyin sun bayyana cewa Shettima ya cancanci zama ministan matasa bisa ayyukan cigaban matasa da ya aiwatar a ƙasar nan

FCT, Abuja - An buƙaci shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya duba yiwuwar naɗa Alhaji Yerima Shettima, shugaban ƙungiyar tuntunɓa ta matasan Arewa na ƙasa (AYCF), a matsayin ministan matasa a gwamnatinsa.

Jaridar The Sun ta rahoto cewa wasu ƙungiyoyi da suka fito daga sassa daban-daban na ƙasar nan, su ne suka yi wannan kiran ga shugaban ƙasar a ƙarƙashin ƙungiyar Nigeria Youth for Peace and Social Justice Forum (NYPSJF).

Kara karanta wannan

Hannatu Musawa Tana Bukatar NYSC Satikifet Domin Zama Minista? Babban Lauya Ya Bayyana Yadda Lamarin Yake

An bayyana wanda yakamata ya zama ministan matasa
An bukaci Shugaba Tinubu ya nada Alhaji Yerima Shettima ministan matasa Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Sun bayyana cewa Shugaba Tinubu yana buƙatar ya duba yiwuwar ba Shettima muƙamin, inda suka ƙara da cewa shugabann na AYCF ya taka muhimmiyar rawa wajen ayyukan matasa a ƙasar nan.

Wasu daga cikin shugabannin ƙungiyoyin waɗanda suka samu wakilcin, Samuel Garry, Ahmed Mohammed Rufai da Christiana Nicholas, sun bayyana cewa Shettima ya yi ta wayar da kai kan zaman lafiya da adalci a yankunan ƙasar nan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shettima ya cancanci zama minista

Ƙungiyoyin suna son Shugaba Tinubu ya kai Shettima kusa da shi ta yadda zai nuna ƙwarewarsa ga ƴan Najeriya da duniya baki ɗaya.

Sun bayyana cewa sun yi wannan kiran ne saboda shugaban ƙasar, ya nuna muhimmancin cancanta da damawa da matasa a cikin gwamnatinsa.

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

"Mun ji a jikinmu cewa nauyi ya rataya a wuyanmu wajen neman shugaban matasa wanda ya cancanta sannan dukkanin yankunan ƙasar nan sun yi amanna da shi domin ya shiga cikin gwamnatin nan.

Kara karanta wannan

"Ba a Taba Yi Ba": An Yabawa Shugaba Tinubu Kan Wani Muhimmin Abu Da Ya Yi Wa 'Yan Kabilar Ibo

Ministan matasa dai na ɗaya daga cikin ministocin da har yanzu Shugaba Tinubu bai naɗa ba, tun bayan da ya hau kan karagar mulki a ranar 29 watan Mayun 2023.

Shehu Sani Ya Caccaki Umahi

A wani labarin kuma, tsohon sanataan Kaduna ta Tsakiya, Sanata Shehu Sani ya yi wa ministan ayyuka, David Nweze Umahi, shaguɓe.

Shehu Sani ya zargi ministan da riƙe muƙamin minista tare da na sanata a lokaci ɗaya. Sani ya yi nuni da cewa Umahi ya riƙe kujerun biyu da hannayensa ne domin gudun ɓacin rana.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng