Obi Vs Tinubu: Malamin Coci Kingsley Okwuwe Ya Ce Peter Obi Zai Amshe Kujerar Tinubu
- Dan takarar jam'iyar Labour a zaɓen shugaban ƙasar da ya gabata ya shigar da ƙara kan zaɓen
- Fasto Kingsley Okwuwe na cocin 'Revival and Restoration Global Mission' ya bayyana wahayin da aka yi masa
- Malamin ya hasaso cewa kotu za ta sauke Tinubu, kuma Peter Obi ne zai maye gurbinsa
FCT, Abuja - Fasto Kingsley Okwuwe na cocin 'Revival and Restoration Global Mission', ya bayyana cewa ɗan takarar shugabancin ƙasa na jam'iyyar Labour wato Peter Obi, zai cika burinsa.
Fasto Okwuwe ya bayyana hakan ne a wani bidiyo da ya ɗora a shafinsa na YouTube.
Peter Obi zai zama shugaban ƙasa
Faston ya bayyana cewa ya gani a wahayin da aka yi ma sa cewa Peter Obi zai zama sabon shugaban ƙasa, a yayin da Najeriya za ta dawo sabuwa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya ce Bola Tinubu zai tafi a yayin da Peter Obi zai zo domin ya ɗare kan kujerarsa.
Ya ƙara da cewa kujerar da Tinubu yake kai a yanzu ba halastacciya ba ce, kuma Peter Obi zai yi nasara kansa a kotu.
Peter Obi dai ya shigar da ƙarar Shugaba Tinubu ne a kotun sauraron ƙararrakin zaɓe, inda yake ƙalubalantar nasarar da ya samu a zaɓen da ya gabata.
Shehu Sani ya ƙalubalanci Atiku kan ci gaba da shari'a Tinubu
A baya Legit.ng ta yi rahoto kan martanin da tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Sanata Shehu ya yi kan karɓar muƙamin da tsohon gwamnan Ribas Nyesom Wike ya yi.
Shehu Sani ya ce bai kamata Atiku Abubakar ya ci gaba da shari'a da Shugaba Bola Tinubu ba tunda ɗan jam'iyyarsu ya karɓi muƙami a gwamnatinsa.
Nyesom Wike dai na daga cikin ministoci 45 da da shugaba Bola Tinubu ya naɗa a matsayin waɗanda za su taya shi tafiyar da gwamnatinsa.
Shugaba Tinubu ya aike da muhimmin sako ga ministocinsa
Legit.ng a baya ta yi rahoto kan gargaɗin da shugaba Bola Tinubu ya aike ga sabbin ministocinsa da ya naɗa.
Shugaba Tinubu ya ce shi da ministocinsa kamar matafiya ne a cikin jirgi ko mota, amma dai shi ne direban.
Asali: Legit.ng