Ana Rigima a Kan Kujerar Minista 1 Da Ta Ragewa Bola Tinubu Ya Nada a Gwamnati
- Matasan APC sun rabu gida-gida dangane da wanda ya fi dacewa ya zama ministan harkar matasa
- Akwai wadanda su ka ce a bar Seyi Tinubu ya zakulowa mahaifinsa wanda ya fi cancanta da matsayin
- Wasu kungiyoyi sun soma tallata Nicholas Felix yayin da wasu ke tare da shugaban matasan APC
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Abuja - Wasu matasa masu ruwa da tsaki a jam’iyyar APC sun samu sabani a junansu kan wanda ya dace ya zama ministan harkokin matasa.
A makon nan ne wasika ta fito daga jagororin matasa da ke jihohin kasar nan, su na ba Bola Tinubu shawarar ya bar wuka da nama hannun Seyi Tinubu.
Shugabannin matasa fiye da 30 su ka sa hannu, su ka nuna ba su goyon bayan a nada Dayo Israel ya zama sabon ministan da zai jagoranci sha’aninsu.
Matasa sun juyawa Israel baya?
Israel wanda shi ne shugaban matasan APC na kasa ya samu goyon mataimakansa; Jamaludeen Kabir, Oluwaseun Oguntade da kuma Mogaji Olatunde.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A sakatariyar APC da ke garin Abuja, rahoto ya zo cewa an ga wasu magoya baya su na rokon Shugaba Bola Tinubu ya ba Nicholas Felix wannan kujera.
Dr. Nicholas Felix wanda ya taba neman shugabancin Najeriya ne mataimakin shugaban majalisar kula da matasa wajen yakin zaben APC a 2023.
Shugaban magoya bayan, Kwamred Ikechukwu Norbert ya ce gwaninsu ya dace da mukamin. Zuwa yanzu ministocin da aka nada sun shiga ofis.
Yarbawan APC su na neman Minista
Wata kungiya ta matasan yarbawa na APC ta fito da wasu sunaye, ta ce daga cikin jagororin jam’iyya na kudu maso yamma za a dauko ministan.
Cire Tallafi: Sauki Ya Zo Yayin Da Tinubu Ya Shirya Siyar Da Litar Gas Naira 250 Madadin Fetur, Ya Tura Bukata Ga 'Yan Najeriya
An kawo Makinde Araoye, Seun Olufemi-White; Ayodele Olawande, Bolaji Afeez Repete, Prince Oyekunle Oyewumi, sai Titilope Ayoka Gbadamosi.
Ragowar sunayen su ne: Ademola Adeyeye, Dayo Israel, Bayo Adenekan da Dr Seriki Muritala.
Wasu kuma su na da ra’ayin cewa Ismael Ahmad ya cancanta da wannan matsayi saboda ya jagoranci matasan jam’iyya, kuma an ga irin kwazon shi.
A Twitter, Olusegun Dada ya nesanta kan sa daga hayaniyar, hadimin shugaban kasar ya ce a kyale Tinubu ya dauko wanda ya ke so ya yi aiki da shi.
Minista: Canzawa Abubakar Momoh ma'aikata
Ana daf da rantsar da ministoci sai aka ji labari shugaban kasa ya dauke Abubakar Momoh daga ma’aikatar matasa, ya maida shi ma'aikatar Neja-Delta.
Legit.ng Hausa ta na sane da cewa Bola Ahmed Tinubu ya nada ministoci 45, kujerar da ta rage ita ce ta harkar matasa, har yanzu ba a nada kowa ba.
Asali: Legit.ng