Tsohon Bidiyon Wike Da Ya Caccaki Buhari Ya Yi Wa 'Yan APC Shagube Ya Janyo Muhawara a Intanet
- Wani tsohon bidiyon Nysome Wike da yake yi wa 'yan takarar jam'iyyar APC shaguɓe ya janyo cece-kuce
- Wike ya bayyana cewa abin kunya ne wani ɗan takarara ya zo yana cewa zai ɗora daga inda Buhari ya tsaya
- Wike ya yi waɗannan kamalai ne a lokacin da ake shirye-shiryen zaɓen shugabanni na 2023
Nyesom Wike a cikin wani tsohon bidiyo ya caccaki salon mulkin APC a lokacin gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.
A cikin bidiyon an jiyo Wike yana wasu kalamai da ke nuni da shaguɓe ga ɗaya daga cikin 'yan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar APC.
IG Wala, ɗan rajin kare haƙƙin bil'adama ne ya ɗora bidiyon a shafinsa na Facebook, inda jama'a da dama suka tofa albarkacin bakunansu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wike ya soki Buhari, ya yi wa 'yan takarar APC shaguɓe
A cikin ɗan gajeren faifan bidiyon, an jiyo Nyesom Wike na cewa bai kamata a halin da ake ciki wani ya zo yana faɗar cewa idan aka zaɓe shi zai ɗora daga inda Buhari ya tsaya ba.
Ya ce abin kunya mutum ya yi iƙirarin ɗorawa daga inda Buhari ya tsaya saboda babu komai cikin mulkinsa sai taɓarɓarewar al'amura.
A kalamansa:
“Idan na ji mutanen da ke takara a APC suna cewa, za su ɗora daga inda Buhari ya tsaya; ta ɓangaren mutuwar mutane a kowace rana, da ta ɓangaren karyewar darajar naira kowace ranar, ina matuƙar jin kunya.”
“Menene wani abin kirkin da Buhari ya yi? Kawo yunwa? Ko ko matsalar tsaro? Ko ko taɓarɓarewar tattalin arziƙi?, wannan ai abin kunya ne.”
Martanin masu amfani da kafar Facebook ga Wike
Biyo bayan wannan tsohon bidiyo na Wike da aka wallafa, masu amfani da kafar sadarwa ta Facebook da dama sun yi ma sa martani kamar haka:
Kotun Zabe: Babban Malamin Addini Shawarci 'Yan Najeriya Kan Abin Da Za Su Yi Idan Kotun Koli Ta Yi Hukunci
Hussaini Umar ya ce:
“Hmmmmmmm”
Yusuf Tukur ya ce:
“Wannan ya iya ya huta ai. Wike ɗan duniya ba”
Nura Bilyaminu Kibiya ya ce:
“Shashashun 'yan siyasa. Suna faɗar gaskiya ne kawai idan ba da su ake damawa ba.”
Ahmed Baba Ahmed ya ce:
“Wannan ai dan' daba suka sungumo kaman kifi.”
Ibrahim Garba Yakubu ya ce:
“Baya da kunya”
Nyesom Wike dai shi ne aka bai wa muƙamin ministan Birnin Tarayya Abuja, a ƙarƙashin gwamnatin Bola Tinubu na jam'iyyar APC.
PDP za ta hukunta Wike da sauran gwamnonin G5
Legit.ng a wani rahoto na daban da ta kawo a baya, kun ji cewa jam'iyyar adawa ta PDP na shirin hukunta tsohon gwamnan Ribas, Nyesom Wike da wasu gwamnonin G5.
Hakan ya biyo bayan naɗin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu na jam'iyyar APC ya yi wa Wike a matsayin ministan Birnin Tarayya Abuja.
Tinubu vs Atiku, Obi: An Gargadi Kotun Zaben Shugaban Kasa Kan Yin Hukuncin Da Zai Haifar Da Rikici a Kasa
Asali: Legit.ng